Cutar maleriya: Afirka tana da kaso 94 na marasa lafiya da kaso 95 na mace-mace

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis Gwamnatin Tarayya ta bayyana kaɗuwarta kan yadda adadin masu kamuwa da cutar maleriya ke hauhawa a Nijeriya.

Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Dakta Iziaq Adekunle Salako ya ce, duk da ƙoƙarin gwamnatoci na tsawon shekaru wajen shawo kan al’amarin, ƙididdiga ta nuna cewa adadin masu cutar sun kai miliyan 263 yayin aƙalla mutane 597,000 suka rasu a sanadiyyar ta a shekarar 2023 a faɗin duniya, inda Afirka take da kaso 94 da kaso 95 na mace-mace.

Ya kuma ce, hauhawar adadin ya sa ake ƙoƙarin ɗaukar matakan gaggawa wajen magance matsalolin da suke haddasa yaɗuwarta acikin al’umma.

Da yake jawabi a zaman rawar da Nahiyar Afirka ke takawa wajen daƙile cutar da haɗin-gwiwar Roll Back Malaria Partnership (RBM) da The African Leaders Malaria Alliance (ALMA), Dakta Salako ya ce akwai takaici a ce ana iya maganin cutar bayan gano ta, amma kuma ta cigaba da zama sababin mutuwar mutane da dama a Nijeriya da ma sauran ƙasashen nahiyar.

Ya ƙara da cewa, duk da ƙoƙarin gwamnati wajen samar da shirye-shiryen yaƙi da cutar, a yanzu abu ne mai wuya a kawo ƙarshenta a nahiyar zuwa nan da 2030.

By Babaji