Daraktan REA, Ahmed Alhasan ya yanki jiki ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Daraktan riƙo na Hukumar Kula da Samar da Lantarki ga Yankunan Karkara REA, Ahmed Alhasan ya yanki jiki ya rasu wajen wani taro, ranar Laraba.

Shugaban hukumar bada kariya ga kwastomomi ta ƙasa, Kunle Olubiyo ya tabbatar da rasuwarsa a wata takardar sakon ta’aziyya.

Ya ce, marigayin ya kai matsayin mataimakin darakta gabanin rasuwarsa, lamarin da ya faru a lokacin da ya halarci taron masu ruwa da tsaki na REA a Jihar Akwa-Ibom.

Rasuwarsa ta sa masu ruwa da tsaki a fannonin lantarki da makamashi suka riƙa miƙa saƙonnin ta’aziyyarsu.

By Babaji