Ba mu samu saƙo a hukumance ba game da ƴan Nijeriyar da aka koro daga Amurka zuwa Ghana ba – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta samu wani saƙo na musamman daga Amurka ko Ghana ba akan rahotannin da ke cewa akwai ƴan Nijeriya daga cikin waɗanda Amurka ta koro zuwa Ghana daga birnin Washington.

Haka na zuwa ne a lokacin da kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewa daga cikin mutane 14 da Amurka ta koro akwai ƴan Nijeriya da ƴan wasu ƙasashen yammacin Afirka a ƙarƙashin shirin karɓarsu a ƙasar kafin kai su ƙasashensu.

Akan haka ne Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa ya shaida wa jaridar News Point Nigeria cewa ba a sanar da Nijeriya batun ba a hukumance, wanda hakan ya sa ba za ta yi wani abu a kai ba.

An samu haka ne yayin da ƴan Nijeriya da dama ke nuna damuwarsu kan yadda ake samun rashin wadataccen sadarwa tsakanin gwamnatocin ƙasashe, lamarin da ka iya haifar da takun saƙa a harkokin dimukraɗiyya.

Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun tsaiko ba game da tsare-tsaren Amurka, inda a watan Yuli, Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ya soki Gwamnatin Shugaba Donald Trump akan yadda ta ke matsa wa ƙasashen Afirka ciki har da Nijeriya wajen karɓar mutanen da ta koro.

By Babaji