13
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni daga ƙasar Burkina Faso sun bayyana cewa, Gwamnatin ƙasar ta sanar da ɗauke kuɗin biza akan dukkan ƴan Afirka da ke son shiga ƙasar domin inganta haɗin kai a shiyyar da bunƙasa walwalar al'umma. Ministan Tsaron ƙasar, Mahamadou Sana ya bayyana haka a wani saƙo ranar Alhamis, bayan wani zama da shugaban mulkin sojin ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traoré. Ya ce, daga yanzu duk wani ɗan Afirka da ke da muradin zuwa Burkina Faso, an sauke masa kuɗin biza. Saidai duk da ci-gaban, matafiya za su riƙa cike fom na neman biza kafin a…
