Babaji

5698 Posts

Wike, Fubara, sarakuna da manyan ƴan siyasa sun ƙi halartar addu’ar bankwana da kantoman Ribas

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Taron addu'ar bankwana da Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas ya shirya ya samu ɗaukewar ƙafa na wasu muhimman mutane a jihar musamman ga rashin ganin Ministan Abuja Nyesom Wike da dakataccen gwamna Siminalayi Fubara. A jiya Lahadi aka gudanar da taron a wani coci da ke Fatakwal, babban birnin jihar yayin da kantoman ya ke shirin barin ofis duba da wa'adin dakatarwar wata shida da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Fubara a watan Maris ya zo ƙarshe. A yayin jawabinsa na bankwana, Ibas ya yi gargaɗin koma wa rikicin siyasa da jihar ta tsinci…
Read More

Rajistar katin zaɓe: Bichi na neman yin fice cikin ƙananan hukumomin Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano ta ƙara azama wajen faɗakar da al'ummarta muhimmancin rijistar katin zaɓe da ake cigaba da gudanarwa a halin yanzu a faɗin Nijeriya. Hakan ya samu ne a sakamakon jajircewa da aiki tuƙuru na shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, kamar yadda wasu daga cikin al'umar yankin suka bayyana. A zantawar da jami'ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta yi da wasu daga cikin al'ummar yankin a Mazaɓar Hagagawa, da dama sun bayyana farin cikinsu ganin yadda aka wayar musu da kai kan…
Read More

Kwara: An samu kuɗaɗen ƙasar waje da wuƙa a hannun mabarata yayin kame

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Kwara ta ƙaddamar da atisayen kamen masu bara a titunan manyan unguwannin babban birninta, wato Ilorin, inda aka kama kimanin mabarata 40 a tsakiyar mako. A yayin haka ne aka ƙwato wasu ababen ban-mamaki da suka haɗa da tsabar kuɗaɗe ciki har da Dalar Amurka da nairorin Nijeriya da jimillar adadinsu ya kai kusan N100,000 da kuma wata wuƙa mai kaifi. Ma'aikatar Walwalar Al'umma da Ci-gaba da haɗin-gwiwar jami'an Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS) reshen jihar suka ƙaddamar da aikin kamen a yankunan Tipper Garage, Tank, Offa Garage da Shataletalen…
Read More

Masanin shari’a ya soki Majalisar Dattawa kan ƙin amince wa komawar Natasha bakin aiki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙwararre akan harkar shari'a, Emmanuel Umahi Ekwe (Esq), ya caccaki Majalisar Dattawa bisa hukuncinta na ƙara wa'adin dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan akan wata shida da aka yi mata tun a watan Maris. A wata sanarwa da ya fitar wa Blueprint a yau Lahadi, Umahi ya bayyana hakan a matsayin abinda aka yi ba bisa doka ba, lamarin da ya kira da saɓa wa dokokin ƙasa da na mulki. A cewarsa, sashi na 66(5) na kundin doka na 1999, ya taƙaice wa'adin dakatarwar da za yi wa jami'an gwamnati, yana mai…
Read More

Ambaliya: Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jihohi 11

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta fitar da saƙon gargaɗi ga al'ummar jihohi 11 sakamakon yiwuwar samun mamakon ruwan sama a tsakanin ranakun Lahadi da Alhamis, lamarin da ka iya haddasa ambaliya da ɗaiɗaita mazauna da gidaje. Cibiyar Gargaɗin Ambaliya akan Lokaci ta Ƙasa (NFEWC) ƙarƙashin Ma'aikatar Kula da Muhalli, ta bayyana jihohin da ambaliya ka iya aukuwa a wasu yankunansu. Jihohin sune: Adamawa, Benuwai, Nasarawa, Taraba, Delta, Neja, Kebbi, Kano, Katsina, Sokoto, da Zamfara. A cewarta, yankunan sun haɗa da:Adamawa: Ganye, NatubiBenuwai: Abinsi, Agyo, Gogo, Ito, Makurdi, Udoma, UkpiamNasarawa: Agima, Rukubi, OdogboTaraba: Beli, Serti, DongaDelta: Umugboma,…
Read More

Likitoci sun janye yajin aiki

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara a ranar Juma'a sakamakon ƙorafe-ƙorafen da suka shafi rashin kulawa da lamuran ƴaƴanta daga ɓangaren gwamnati. A wata sanarwa da NARD ta fitar, ta ce ta janye yajin aikin na kwana biyar ne bayan Gwamnatin Tarayya ta amince da fara biyan wasu daga cikin buƙatunsu. "Bayan yunƙurin da gwamnati ta nuna na biyan wasu buƙatun da muka sanar, da kuma shirin fara biyan alawus ga ma'aikatan da ke bin bashi…mun amince mu janye yajin aikin daga ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi," inji sanarwar. Ta…
Read More

Kebbi: Majalisar Dokoki ta yi watsi da zargin ɗaukar nauyin tashin-tashina da Malami ya yi akan gwamnan jihar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dokoki a Kebbi ta yi tir da ƙorafin da tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya shigar akan Gwamna Nasir Idris, inda ya zarge shi da shigo da ƴan daba da sojojin haya daga waje domin haddasa tarzoma a jihar. Da yake ganawa da manema labarai a farfajiyar majalisar, Kakakinta, Hon. Muhammad Usman ya bayyana zargin Malamin a matsayin zance mara asali da aka kiekida nufin ruɗar da al'umma. Hon. Usman ya ce, jihar Kebbi waje ne da ke da daraja da kima a idon al'umma a matsayinta na ɗaya…
Read More

Abuja: Sun daɓa wa ɗan Jamus wuƙa bayan masa fashi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu miyagu a babura sun daɓa wa wani bajamuse wuƙa tare da yi masa fashi a Birnin Tarayya Abuja. A cewar SaharaReporters, wani rahoton tsaro ya bayyana cewa al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na safiyar Asabar akan titin IBB way, kusa da makarantar firamare ta Maitama. Ɗan Jamus din, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya haɗu da iftila'in ne a lokacin da ya ke tafiya a gefen hanya a ƙafa, inda wasu ƴan daba a babura suka cimmasa. An gano cewa, sun caka masa wuƙa sannan suka jefar da shi…
Read More

Ribas: An fara shirye-shiryen koma wa mulkin dimukraɗiyya a jihar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Ribas ta fara gudanar da shirye-shiryen koma wa mulkin dimukraɗiyya daga na dokar ta-ɓaci a jihar. Sakataren gwamnatin, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya sanar da haka a wata takarda. A cewarsa, an gayyaci baki ɗaya masu ruwa da tsaki zuwa interdenominatuonal church thanksgiving service a yau Lahadi. Waɗanda aka gayyata sune manyan sakatarori, ciyamomin ƙananan hukumomi, jagororin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, jagororin hukumomi da sauransu. Kantoman jihar, Ibok-Ete Ibas shi ne baƙo na musamman a taron.
Read More

Nijeriya na cikin ƙasashen Afirka 16 da Amurka ta yi wa ƴaƴanta gargaɗin shiga

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Amurka ta sanya ƙasashen Afirka 16 ciki har da Nijeriya a sahun waɗanda akwai barazanar shiga ga ƴaƴanta a watan nan na Satumba. Ta ce, ta yi haka ne saboda ankarar da mutanenta da ke ƙasashen da masu niyyar tafiya sakamakon samun barazanar tsaro, rikicin siyasa da haɗarin kula da lafiyarsu a ƙasashen. Ma'aikatar Harkokin cikin gida na Amurka ta bad gargaɗin ne a matakai huɗu da suka haɗa da kulawa yadda ya dace kafin yanke shawarar tafiya zuwa matakin ƙarshe da ya shawarci da kada a yi tafiyar saboda barazana ga rayuka.…
Read More