Babaji

5698 Posts

Saudiyya ta sako ƴan Nijeriya uku da aka yi wa cunen miyagun ƙwayoyi bayan Gwamnatin Tarayya ta tsoma baki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumomi a Saudiyya sun sako matafiya uku da aka tsare su bisa zargin su da hannun a ayyukan safarar miyagun ƙwayoyi. Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA, ta sanar da haka a taron manema labarai yau Laraba, inda ta ce an sako Maryam Hussaini Abdullahi, Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddieq bayan shafe makonni huɗu a ɗaure. Daraktan yaɗa labarai na NDLEA, Femi Babafemi ya ce an yi nasarar haka ne bayan da aka ɗauki tsawon makonni ana tattaunawa tsakanin NDLEA, Gwamnatin Tarayya da Hukumar Kula da Lamuran miyagun ƙwayoyi na Saudiyya.…
Read More

Ambaliya: Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jihohi 14

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta yi aiken sabon saƙon gargaɗi da al'ummomin garuruwa 52 a jihohi 14 da ke sassan Nijeriya. Ta yi haka ne domin ankarar da su game da yiwuwar aukuwar ambaliya a tsakanin ranakun 16 da 18 na Satumba, 2025, inda ta kiraye su da shirya wa al'amarin. Cibiyar Gargaɗin Ambaliya akan Lokaci ta Ƙasa (NFEWC) ƙarƙashin Ma'aikatar Kula da Muhalli a wani rahoto da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan kula da lamuran ambaliya da yankunan ruwa Usman Abdullahi Bokani, ta bada gargaɗin tare da kira ga gwamnatocin jihohi, hukumomi da yankuna…
Read More

Tinubu ya dawo Nijeriya bayan kammala hutu a Turai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Talata Shugaba Bola Tinubu ya koma Abuja bayan kammala hutunsa na shekara a Nahiyar Turai. Da fari ya sauka ne a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja inda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa suka marabce shi. Haka kuma, daga ciki akwai Shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila da Ministan Tattali Wale Edun. Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da dawowar Shugaban Ƙasar a wata sanarwa ta ranar Litinin inda ya ce shugaban ya kammala hutun nasa, sannan ana sa ran…
Read More

Babu alamar kawo ƙarshen yunwa da talauci a gwamnatin Tinubu, inji Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa game da halin da ƴan Nijeriya ke ciki na tsananin yunwa da talauci, yana mai gargaɗi cewa hakan na iya janyo rikice-rikicen zamantakewa a ƙasar. A sanarwa da ya fitar ranar Litinin, ya ce rayuwar yawancin ƴan ƙasa ta taɓarɓare kuma hakan na haifar da matsanancin rashin jin daɗi ga al'umma, wanda ke iya barazana ga zaman lafiya da ɗorewar dimukraɗiyya a ƙasar. Atiki Abubakar ya kuma ce rashin tsari mai kyau a harkokin tattalin arziƙi da rashin kulawa daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya na daga cikin abubuwan da ke haifar da…
Read More

Al’umma sun samu sa’ida bayan hauhawar farashi ya ragu da kaso 20 a Agusta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ana sa ran al'ummar Nijeriya su samu sauƙi a farashin kayayyaki yayin da ƙididdiga ta nuna matakin hauhawar farashi ya ragu da kaso 20 a watan Agusta a Nijeriya. Wannan shi ne wata na biyar a jere da ake samun ragi a matakin hauhawar farashin a ƙasar. A cewar, rahoton ofishin kula da sauyin farashi da cibiyar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar a ranar Litinin, hauhawar farashi ya sauko da kaso 20.12 a watan Agusta, 2025 daga kaso 21.88 da aka samu a watan Yuli. Hakan na nuna an samu saukar farashi da…
Read More

Cire tallafin fetur ya ceci Nijeriya daga talaucewa, inji Sarki Sanusi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Muhammad Sanusi II, ya ce cire tallafin man fetur a Nijeriya ya taimaka wajen ceto ƙasar daga shiga matsanancin talauci. Da yake jawabi a babban taron marubuta na Kano International Poetry Festival (KAPFEST) Sarki Sanusi ya bayyana rashin cire tallafin fetur ga gwamnatocin baya a matsayin abinda ya haifar da koma-baya ga asusun gwamnatocinsu. Ya bayyana cewa, tsarin ya tilasta wa gwamnati iya ɗaukar ƙalubalen sauye-sauyen farashin mai a kasuwannin duniya, rashin tsayuwar farashin cinikayya, tsadar sufuri da kashe-kashe a tacewa. A cewarsa, tsarin yana…
Read More

Ba za a dakatar da asusun bankunan ƴan Nijeriya ba saboda rashin lambar haraji – JTB

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Haɗaka ta Haraji JTB, ta ƙaryata rahotannin da ke cewa za a dakatar da asusun bankuna na ƴan Nijeriyar da ba su da lambar haraji, wato Tax ID daga ranar 1 ga Janairun 2026. Hakan na zuwa ne bayan da Kwamitin Shugaban Ƙasa akan Kasafi da Gyare-gyaren Haraji ya fitar da wani kundi, wanda a ciki akwai batun cewa ta yiwu waɗanda ba su da Tax ID su rasa damar gudanar da asusun bankuna, tsare-tsaren inshora, kuɗaɗen fansho of kuma lamuran zuba jari bayan kwanan watan da aka bayyana. A wata takarda da…
Read More

Kotu ta ƙi amince wa buƙatar Nnamdi Kanu ta koma wa Asibitin ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Litinin Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta soke buƙatar da mai fafutukar kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu ya nema domin ba shi izinin ficewa daga hannun hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) zuwa Babban Asibitin ƙasa don matsalar lafiyarsa ta gaggawa. Mai Shari'a Musa Liman, wanda ya yi hukunci kan takardar buƙatar ya ce wa'adinsa na gajeren zango a matsayinsa na Alƙali a kotun ya ƙare a ranar, don haka ba shi da hurumin yin hukunci akan al'amarin. Saboda haka ya umarci a mayar da shari'ar zuwa ga kumdin ƙararraki domin bai…
Read More

KEDCO ya yi bayani kan dalilin yanke lantarkin Asibitin Aminu Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya sanar da kammala warware matsalolin da suka haifar da yanke wuta a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da ke Jihar Kano. A wata sanarwa daga KEDCO kamar yadda NigerianTracker ta ruwaito, al'amarin ya samo asalin ne daga ƙoƙarin raba layin lantarkin farfajiyar asibitin da ɓangarorin bada magani ga marasa lafiya daga sashen gidajen ma'aikatan asibitin. An haɗa na farfajiyar asibitin da ɓangarorin kula da lafiyansa ne da tashar lantarki na 33kV Zaria Road, wanda ke bada wuta na jimillar sa'o'i 22 a kullum. Hukumar gudanarwar…
Read More

Yanke wuta ya haifar da mace-mace a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da ke Jihar Kano ya miƙa saƙon neman agajin gaggawa ga Kamfanin Raba Wutar Lantarki na jihar (KEDCO) da ya gaggauta warware matsalar katsewsr wuta a asibitin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikin marasa lafiya. A wata sanarwa da Shugabar sashen yaɗa labarai na AKTH, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar, hukumar gudanarwar asibitin ta bayyana damuwarta kan yadda hakan ke jefa al'umma cikin ƙunci. "Hukumar gudanarwar AKTH tana alhinin rasuwar wasu marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali bayan KEDCO ya katse wutar lantarki…
Read More