
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Muhammad Sanusi II, ya ce cire tallafin man fetur a Nijeriya ya taimaka wajen ceto ƙasar daga shiga matsanancin talauci.
Da yake jawabi a babban taron marubuta na Kano International Poetry Festival (KAPFEST) Sarki Sanusi ya bayyana rashin cire tallafin fetur ga gwamnatocin baya a matsayin abinda ya haifar da koma-baya ga asusun gwamnatocinsu.
Ya bayyana cewa, tsarin ya tilasta wa gwamnati iya ɗaukar ƙalubalen sauye-sauyen farashin mai a kasuwannin duniya, rashin tsayuwar farashin cinikayya, tsadar sufuri da kashe-kashe a tacewa.
A cewarsa, tsarin yana nufin ƴan Nijeriya za su riƙa sayan fetur a ƙasa da farashin da ake sayo shi a kasuwa yayin da gwamnati take cike gurbin abinda aka rasa ko nawa ya kai a kasuwannin mai na duniya.
“Kaɗai abinda tallafi yake nufi, gwamnati tana cewa idan fetur N100 ne, ƴan Nijeriya za su biya N70, sannan ni kuma zan biya N30”, inji Sarki Sanusi.
Kazalika, Sarkin ya kuma soki gwamnatocin baya akan gaza gyara matatun mai na gwamnati, yana mai cewa matatun waje su ke amfana da tallafi tare da rasa ayyuka daga harkar tattalin arziƙin Nijeriya.
