19
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata kotun sojoji da ke sansanin Maxwell Khobe a Jos, Jihar Filato, ta yanke wa wani soja da ke aiki a runduna ta 3, wato Private Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya. An yi masa hukuncin ne sakamakon samun sa da laifin halaka wani ɗan adaidaita sahu mai suna Abdulrahman Isa a garin Azare da ke Jihar Bauchi. Birgediya Janar Liafis Bello, wanda ya yi hukuncin a ranar Alhamis, ya ce an samu sojan da laifin kisa da mallakar alburusai ba bisa doka ba. An gurfanar da Musa ne bayan gano cewa shi…
