Filato: Za a rataye soja kan kisan ɗan sahu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata kotun sojoji da ke sansanin Maxwell Khobe a Jos, Jihar Filato, ta yanke wa wani soja da ke aiki a runduna ta 3, wato Private Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yi masa hukuncin ne sakamakon samun sa da laifin halaka wani ɗan adaidaita sahu mai suna Abdulrahman Isa a garin Azare da ke Jihar Bauchi.

Birgediya Janar Liafis Bello, wanda ya yi hukuncin a ranar Alhamis, ya ce an samu sojan da laifin kisa da mallakar alburusai ba bisa doka ba.

An gurfanar da Musa ne bayan gano cewa shi da wani mai suna Oba sun gayyaci ɗan sahun zuwa gidansa da nufin taya su matsar da wasu kayayyaki.

Hujja ta bayyana cewa, sojan ya buga wa mamacin itace ne kana daga bisani ya shaƙe masa wuya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Daga lokacin ne ya ɗauki gawar tare da sanya ta acikin wani buhu, sannan ya jefar da ita a tsakanin ƙauyukan Shira da Yala.

Haka kuma, kotun ta gano cewa Musa ya mallaki waɗansu alburusai guda 34 ƙirar 7.62mm ba bisa ƙa’ida ba.

Da yake gabatar da hukuncin, Janar Bello ya bayyana ɗanyen aikin sojan a matsayin abinda aka yi bisa rashin tausayi, wanda kuma saɓa wa dokokin sojoji ne da tsarin doka akan aikin soja na bai wa rayukan ƴan ƙasa kariya.

By Babaji