Isra’ila tana kashe Falasɗinawa ba gaira ba dalili, inji Sanatan Amurka, Bernie Sanders

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen Sanatan Amurka, Bernie Sanders ya bayyana kisan kiyashin Isra’ila akan mutanen Gaza a matsayin zalunci, inda ya jaddada kira ga Washington da ta tsame hannunta a ciki.

A ranar Laraba Sanatan ya bayyana haka bayan hukumar tuntuɓa ta Amurka ta fitar da rahoton da ke nuna Isra’ila na kisan kiyashi na babu gaira babu dalilin a zirin Gaza.

Santan Amurkan ya bada misali da kalaman manyan jami’an Isra’ila na kira da a tarwatsa Gaza tare da shafe ta a doron ƙasa da baki ɗaya al’ummarta.

Tsohon takarar shugaban ƙasar, wanda kuma jagora ne a tafiyar siyasar Amurka, shi ne Sanatan ƙasar na farko da ya kira yaƙar Gaza da Isra’ila ke yi a matsayin kisan kiyashi. Da dama daga ƴan Majalisar Wakilan ƙasar sun yi haka a baya.

Hakan ya nuna yadda Isra’ila ta yi buris da dokokin yaƙi na ƙasa-da-ƙasa da ƙoƙarin take dukkan sharuɗɗan yaƙi da dokar ta ayyana a ƙoƙarinta na shafe Falasɗinawa daga doron ƙasa, laifin da shi ne mafi girma a ƙarƙashin dokokin ƙasa-da-ƙasa.

Ya kuma yi gargaɗin hakan ka iya faɗaɗa zuwa wasu yankunan shiyyar, inda ya ce yana fargabar kada hakan ya zama sanadin duniya ta tsinci kanta a hali na rashin tausayi ko jinƙai a tsakanin ƙasashe da al’ummominsu.

By Babaji