Magidanci da matarsa da ɗiyarsa sun kuɓuta bayan biyan Naira miliyan 50

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Matashin ɗan kasuwa a Katsina, Anas Ahmadu da matarsa Halimatu mai ɗauke da juna biyu wata bakwai da ɗiyarsu mai shekaru biyu da aka yi garkuwa da su, sun shaƙi iskar ‘yanci.

An sako mutanen ne a daren ranar Laraba bayan sun shafe kwanaki 21 a tsare a hannun ‘yan bindiga, kamar yadda wani ɗan uwan iyalan ya tabbatar wa manema labarai.

Ɗan uwan, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an biya kuɗin fansa naira miliyan 50 domin a sako su.

“Alhamdulillah! A daren nan masu garkuwa da su sun sako Anas, Halimatu da ‘yarsu, suna kan hanyarsu ta komawa gida, amma an biya kuɗin fansa Naira miliyan 50 ga ɓarayin.” Inji shi.

Ya ƙara da cewa, saboda dalilai na tsaro, ba za a bayyana cikakken bayanin wurin da aka ɗauko waɗanda aka yi garkuwar da su.

Blueprint Manhaja ta rawaito ce an sace magidanci da iyalansa a ranar 26 ga Agusta, 2025, bayan ‘yan bindiga sun kai masu farmaki a gidansu da ke Filin Canada Quarters, cikin birnin Katsina.

Da farko dai masu garkuwa da mutanen sun buƙaci a biya su Naira miliyan 600 kafin sakinsu, amma daga baya sun rage kuɗin fansar zuwa Naira miliyan 100 sai dai daga bisani ɓarayin dajin sun rage kuɗin zuwa Naira miliyan 50.

By ukarofi