Gwamnatin Tarayya ta raba jimillar biliyan N330 ga magidanta miliyan 8.1 a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta raba jimillar Naira biliyan 330 ga ƴan Nijeriya su guda miliyan 8.1 a ƙarƙashin shirinta na ‘National Safety Net Programme’ (NSSNP), lamarin da jami’ai suka bayyana a matsayin gagarumar hanyar tallafa wa al’umma a tarihin Nijeriya.

A ranar Laraba Ministan Kuɗi da Tattali , Wale Edun ya bayyana haka a Abuja a lokacin da yake sharhi kan wani zama da kwamitin shugaban ƙasa akan zuba jari ga al’umma da Shugaba Bola Tinubu ya kafa a farkon wannan shekarar.

Ya ce, an samar da shirin ne domin rage raɗaɗi ga al’umma duba da dauko hanyar gyare-gyare a tattali da cire tallafin fetur da Shugaban ƙasar ya yi, lamarin da ya jefa al’umma da dama cikin matsin rayuwa.

Ya bayyana cewa, kimanin mutane miliyan 8.1 suka amfana da shirin zuwa yanzu, waɗanda kowannensu ya samu N25,000 inda kuma suke jiran samun ƙarin wasu kuɗaɗen a nan gaba.

Ya ƙara da cewa, amfani da lambobin NIN da BVN ya taimaka wajen daƙile damfara da siyasantar da al’amarin.

Haka kuma, an tantance magidanta miliyan 2.2 sannan an biya su ta asusun bankunansu kai-tsaye a zango ƙarshe na shirin.

Kazalika, shirin ya samu tallafin Dala miliyan 800 daga Bankin Duniya da nufin harin magidanta miliyan 15 zuwa miliyan 19.7, wanda zai wakilci ƴan Nijeriya aƙalla guda miliyan 70.

By Babaji