20
Sep
An yi kira ga ɗaukacin al'ummar ƙananan hukumomin Jihar Kano da su yi koyi da Ƙaramar Hukumar Bichi wajen saka kishin yankinsu ba tare da bambancin siyasa ba. Shugaban kasuwar zamani ta Bichi, Alhaji Garba Tukur ne ya bayyana haka yayin tattaunawarsa da jami'ar yada labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo. Alhaji Garba Tukur ya ce, kishin juna da haɗin kai na al'ummar Bichi ya kawo ci-gaba da bunƙasar karamar hukumar duba da ayyukan gani da ido da bambanci na siyasa bai hana ta rabauta da su ba waɗanda suka hada da; gina babbar kasuwa da samar da wutar…
