Babaji

5698 Posts

Legas: ‘Yan sanda sun cin zarafin ɗan jaridar ɗaukar hoto na Blueprint, Essiet da tsare shi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani ɗan jaridar ɗaukar hoto na jaridar Blueprint mai suna Sunday Essiet ya tsinci kansa a mawuyacin hali yayin da jami'an Taskforce na kula da muhalli a Jihar Legas suka lakaɗa masa duka. Sun kuma tsare shi na tsawon sa'o'i 10 a lokacin da yake bakin aiki. Al'amarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar, a yankin rukunin gidaje na Jakande yayin da jami'an ke gudanar da wani aiki. Mista Essiet ya bayyana cewa, sai da ya samu umarnin ɗaukar rahoton aikin jami'an daga wani babban jami'in ƴan sanda kafin ya fara aikin. A…
Read More

Alƙalin alƙalai za ta rantsar da lauyoyin SAN 57 yayin da Kotun Ƙoli ke shiga sabuwar shekarar shari’a

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Kudirat Kekere-Ekun za ta rantsar da sababbin manyan lauyoyin Nijeriya, wato SAN guda 57. Taron ɓangare ne na shirye-shiryen zagayowar zangon 2025/2026 na shekarar shari'a. Ana sa ran gudanarwa a farfajiyar kotu ta Kotun Ƙoli, kamar yadda Daraktan Hulɗa da jama'a na Kotun Ƙoli, Festus Akande ya bayyana a Abuja cikin wata takarda. Haka kuma ana tsammanin ganin manyan alƙalai a ɓangaren harkar shari'a su gabatar da jawabai musamman kan ababen da suka shafi matakin fannin nasu. Kazalika, za a fara ne da misalin ƙarfe 10 na safe,…
Read More

Mutane bakwai sun rasu yayin da 67 suka kamu da cutar fata a Adamawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da bincike akan wata sabuwar cutar fata da ta ɓulla, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane bakwai bayan da dama sun kamu da ita a wani ƙauyen Jihar Adamawa. Kodinetan riƙo na shirin kula da cutukan tarin fuka, fata da sanyi mai tsanani, Dakta Adesigbin Olufemi ya tabbatar da al'amarin a wata hira da manema labarai, ranar Lahadi. A cewarsa, zuwa 10 ga watanni Satumba an samu tabbacin mutane 68 sun kamu da cutar, inda takwas daga ciki nasu ya yi tsanani waɗanda a yanzu suke Asibitin Koyarwa na…
Read More

An kama shi a Kano kwanaki da yi wa babban mawaƙi fashi a Legas

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano, ta ce ta yi nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannun a laifin fashi da yunƙurin kisa ga wani sanannen mawaƙi a Nijeriya, wato Lil Kesh da wani mazaunin Legas. Kakakin ƴan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da haka a wata takarda, inda ya ce hakan ya samu ne a ranar 11 ga watan Satumba sakamakon aikin bin diddigi da jami'ai suka yi bayan samun wasu bayanan sirri. Waɗanda aka kaman sune Matthew Adewale mai shekaru 25 da wani Mukhtar Muhammad ɗan shekara…
Read More

Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 80

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) karo na 80 da za a yi a birnin New York da ke Amurka. Za a gudanar da shi ne daga ranar Litinin, 22 zuwa Lahadi, 28 ga Satumba, 2025. A sanarwar da Kakakinsa Stanley Nkwocha ya fitar, ya ce za a yi haka ne bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu. Shettima zai gabatar da jawabi a madadin Nijeriya ranar Laraba, 24 ga Satumba a tsakanin ƙarfe 3 na rana zuwa 9 na dare agogon New York. Haka kuma…
Read More

Rundunar soji ta umarci a yi bincike kan fashewar bom a masana’antar makaman tsaro ta Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar sojoji ta ƙaddamar da aikin gudanar da bincike akan tashin bom da ya faru a masana'antar makaman sojoji (DICON) da ke Kaduna, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya da raunata wasu da dama. Lamarin ya auku ne a safiyar jiya Asabar inda ya sa al'umma a yankunan kusa da wajen cikin tsoro da zaman ɗar-ɗar. Shaidu sun bayyana al'amarin a matsayin abin tsoro da firgitarwa saboda da yadda aka ji ƙara sassa da dama na birnin Kaduna. A wata takarda da Daraktan yaɗa labaran Hedikwatar Tsaro (DHQ), Birgediya Janar Tukur Gusau ya…
Read More

Sakkwato: Lakurawa sun halaka mai gari da wani kan shiga bijilante a Tangaza

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mutum ɗaya tare da mai gari a Ƙauyen Sanyinna da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato sun rasu yayin da wasu da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka farmaki ƙauyen a ranar Alhamis. Mai taimaka wa Shugaban ƙaramar akan lamuran tsaro, Garzali Raccah ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce maharan sun je ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare inda suka buɗe wa jama'a wuta gabanin zuwa gidan mai garin. Ya bayyana cewa, wani ɓangare na Lakurawa ya gargaɗi mazauna ƙauyuka da kada su shiga aikin bijilante, lamarin da suka…
Read More

DA ƊUMI-ƊUMI: Mutane biyu sun rasu a fashewar bom a masana’antar makaman sojoji a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mutane biyu sun rasa rayukansu a lokacin da wani abin fashewa ya tarwatse a masana'antar makaman sojoji (DICON) da ke yankin Kakuri a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna. Rahotanni sun bayyana cewa, an jiyo ƙarar tashin dom ɗin a da dama daga unguwannin birnin ciki har da Chikun da Kaduna ta Kudu a safiyar yau Asabar. Haka kuma jama'a da dama sun jikkata yayin faruwar al'amarin, wanda kawo yanzu ba a san musabbabinsa ba. Tuni aka garzaya da waɗanda suka raunata zuwa asibitoci mafi kusa da wajen da abin ya faru. A…
Read More

Abinda ya sa na zaɓi zaman lafiya akan siyasa – Fubara kan dokar ta-ɓacin Ribas

Gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya bayyana cewa saboda buƙatar zaman lafiya ya sa bai ƙalubalanci ayyana dokar ta-ɓaci ba a jiharsa, wanda hakan ya yi sanadin dakatar da gwamnatinsa na tsawon wata shida. A watan Maris Shugaba Bola Tinubu ya sa dokar, wadda ta ƙare a ranar Larabar da ta gabata, lamarin da ya dawo da gwamnan da majalisar dokokin jihar bakin aiki. Da yake jawabi ta kafar talabijin, Siminalayi Fubara, ya ce zai fuskanci lamuran mulki ne don cigaba ta hanyar shimfiɗa ayyukan raya ƙasa da zaman lafiya tsakaninsa da sauran zaɓaɓɓun jami'an gwamnati. Fubara ya kuma yaba…
Read More

Cutar Mashako: An yi kira ga al’ummar Bichi su kai ʼyaʼyansu rigakafi

KƘaramar ukumar Bichi ta yi jan hankali ga iyaye da sauran al'ummar yankin da su riƙa kai ƴaƴansu riga-kafi da kuma gaggauta kai su asibiti idan cutar mashako ta kama su. Shagaban Shashen Lafiya a yankin, Kabiru Abubakar Gwarzo ne ya yi jan hankalin a lokacin da yake ƙarin haske kan iftila'in cutar da ta ɓullar a wasu yankunan jahar ciki har da Ƙaramar Hukumar ta Bichi. Abubakar Gwarzo, ya bayyana cewa da samun rahoton cutar ta ɓulla a wani sashi na Karamar Hukumar ta Bichi, ba tare da bata lokaci ba, aka tura jami'an lafiya yankin da abin ya…
Read More