22
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Amurka ta fitar da sabon gargaɗi ga gurɓatattun mutane ciki har da wasu manya a Nijeriya da ka iya fuskantar takunkumin samun bizar shiga ƙasar, a wani yunƙuri na yaƙi da rashawa a mataki na duniya. Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya a wani shirin wayar da kan al'umma ta #VisaWise TravelSmart, ya ce an ɗauki matakin ne da nufin taimaka wa kauce wa shiga ayyukan rashawa da tabbatar da gaskiya da adalci akan waɗanda suka ci amanar shugabanci da dokar ƙasa. Ƙasar ta kuma ce dokar ba akan iya masu irin laifin kaɗai…
