Babaji

5698 Posts

An yanke wa sojoji hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar wa ƴan ta’adda makamai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yunƙuri na tsaftace ayyuka acikin jami'an sojoji, wata kotun sojoji da ke Maiduguri ta yanke wa wasu sojoji guda huɗu hukunci bisa samun su da hannu a cinikayyar makamai da alburusai tsakanin su da ƴan ta'adda. Rahotanni sun bayyana cewa hukuncin, wanda aka yi a sashen jami'an atisayen Haɗin Kai na hedikwatar rundunar, ya aika saƙon gargaɗi ga dukkan jami'an tsaro da suke taimaka wa abokan gaba. Birgediya Janar Mohammed Abdullahi, wanda ya gabatar da shari'ar ƙarƙashin jagorancin Janar Ugochukwu Unachukwu, ya ce jami'an sun wulaƙanta kakinsu sannan sun ci amanar ƴan…
Read More

Filato: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan majalisa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni daga Jihar Filato sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar mazaɓar Pankshin ta Kudu, Hon. Denty Laven. A cewar rahotannin, an yi garkuwa da shi ne a gidansa da ke yankin Dong a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Jihar Filato na fuskantar ƙalubale a fannin al'amuran tsaro a ƴan kwanakin nan, inda haka ya sa jami'an tsaro suke ta ƙoƙarin shawo kan al'amarin. A makon da ya gabata ƴan bindiga suka shiga unguwar, inda suka yi garkuwa da ɗan hidimar ƙasa na NYSC…
Read More

Yadda DSS ta gayyaci Malami kan harin tawagar motocinsa a Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar ƴan sandan farin kaya DSS, ta gayyaci tsohon Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Ibrahim Malami akan mummunan harin da aka kai wa tawagar motocinnsa a Birnin Kebbi, farkon watan nan. Rahotanni sun bayyana cewa, Malami, wanda shi ke jagorantar tafiyar jam'iyyar ADC a Jihar Kebbi, an masa tambayoyi ne a ofishin DSS na jihar da ke Birnin Kebbi. Al'amarin ya faru ne a lokacin da Malami da tawagarsa ke komawa daga gida bayan sun je ta'aziyyar rasuwar Babban Limamin Masallacin Juma'a na Dakta Bello Halliru. A yayin haka ne aka lalata…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dattawa ta buɗe ofishin Natasha bayan wata shida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawa ta buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke sashe na 2.05 a majalisar. Mataimakin Daraktan majalisar, Alabi Adedeji ya yi haka a yau Talata, lamarin da ya ba Sanatar, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya damar komawa bakin aiki a ranar 7 ga watan October, 2025. A watan Maris, 2025 aka dakatar da ita bayan rikici da zauren majalisar akan batun wajen zama da aka ware mata a ranar 20 ga watan Fabarairu, 2025. Majalisar ta zarge ta da taka dokar tsayuwa sannan ta dakatar da ita na tsawon watanni shida, lamarin…
Read More

UNGA: Shettima ya tallata damar zuba jari a makamashin Nijeriya na Dala biliyan 200

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana wa masu zuba jari na ƙasashen waje cewa Nijeriya na da damar zuba jari mai darajar sama da dala biliyan 200 a fannin makamashi. Shettima ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da Ƙungiyar Kasuwanci ta Ƙasa da Ƙasa (Business Council for International Understanding – BCIU) ta shirya a birnin New York, Amurka, gabanin taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Shettima ya ce, Nijeriya na buƙatar haɗin gwiwa da abokan hulɗa domin cin gajiyar wannan dama, musamman a fannonin makamashi na zamani. Ya ce Nijeriya na da mai da iskar gas…
Read More

Gwamnan Kano ya yi wa Ma’aikatar Shari’a garambawul

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da yi wa wasu jami'an gwamnatinsa garambawul. A wata sanarwa da Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, matakin na ɗaya daga cikin ƙoƙarin da ake yi na inganta harkokin mulki a jihar. A umarnin da Gwamna ya bayar Antoni-Janar kuma kwamishinan shari’a, Barista Haruna Isa Dederi an mayar da shi Ma'aikatar Sufuri yayin da Babban Lauya kuma Babban Sakataren Ma'aikatar Barista Mustapha Nuruddeen Muhammad ya koma Ma’aikatar muhalli a matsayin babban sakatare. Shi kuwa Kwamishinan Harkokin Jinƙai, wanda ya riƙe muƙamin mai riko Ma’aikatar Sufuri, zai…
Read More

NRC ta gano gudu sama da kima da kuren ɗan-adam ne sababin gocewar jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Tashoshin Jiragen ƙasa NRC, ta ce kuren ɗan-adam, gudu sama da kima da rashin aiwatar da tsarin agajin gaggawa a lokacin da ya dace sune dalilan gocewar jirgin Abuja zuwa Kaduna. A ranar 26 ga watan Agusta, 2025 al'amarin ya auku jim-kaɗan bayan tashin jirgin daga Abuja, lamarin da ya raunata fasinjoji 22 da jefa ɗaruruwa cikin firgici. Darakta-Manaja na NRC Dakta Kayode Opeifa ya sanar da haka a wata takarda ranar Litinin, bayan kammala bincike akan al'amarin. Shaidu sun bayyana hatsarin a matsayin abin firgici da ban tsoro musamman bisa…
Read More

Za a fara garƙame iyayen da ba sa son saka yaransu a makaranta – Gwamnatin Gombe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Gombe ta ce za ta fara gurfanar da iyaye da masu jiɓintar lamuran yara bisa rashin sanya su a makaranta. Shugaban Hukumar Ilimi na Bai-ɗaya ta jihar (SUBEB), Babaji Babadidi ya faɗi haka a ranar Litinin, yayin ƙaddamar da shirin wayar da kan al'umma akan saka yara a makaranta a yankin Amada na Ƙaramar Hukumar Akko da ke jihar. Ya ce, akwai yiwuwar iyayen da aka samu da aikata laifin su fuskanci zuwa gidan yari na watanni biyu ƙarƙashin sashe na 19(2) na dokar SUBEB gyarar 2021. Babadidi ya bayyana cewa, an…
Read More

Tinubu ya yi ganawar sirri da Fubara a Abuja bayan dokar ta-ɓaci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Bola Tinubu ya yi wata ganawa ta sirri da Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas a Fadar Shugaban Ƙasa, karo na farko tun bayan kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci a jihar. Hakan na zuwa ne tun komawa bakin aiki da Fubara ya yi a ranar 19 ga watan Satumba, 2025, bayan an ɗage dokar ta-ɓaci da Shugaba Tinubu ya sa a jihar watanni shida da suka gabata. Dokar, wadda aka sa a watan Maris, an soke ta ne a makon da ya gabata bayan burin Tinubu na dawo da zaman lafiya da ɗorewar al'amura…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Ousmane Dembele na PSG ya lashe Ballon d’Or ta 2025

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Paris Saint Germain ya lashe kyautar Ballon d'Or ta shekarar 2025. An gudanar da taron ne a yau Litinin, 22 ga Satumba a ɗakin taro na "the Theatre du Chatelet' a Paris. Dembele ya doke matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal da takwaransa na ƙungiyar, wato Raphinha, kamar yadda ya sha gaban abokansa na PSG, Vitinha da Achraf Hakimi. Ƙwallaye 35 ya ci wa PSG a kakar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadin ta lashe kofunan gida guda uku da na gasar zakarun Turai UEFA Champions League,…
Read More