Tinubu ya yi ganawar sirri da Fubara a Abuja bayan dokar ta-ɓaci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Bola Tinubu ya yi wata ganawa ta sirri da Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas a Fadar Shugaban Ƙasa, karo na farko tun bayan kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci a jihar.

Hakan na zuwa ne tun komawa bakin aiki da Fubara ya yi a ranar 19 ga watan Satumba, 2025, bayan an ɗage dokar ta-ɓaci da Shugaba Tinubu ya sa a jihar watanni shida da suka gabata.

Dokar, wadda aka sa a watan Maris, an soke ta ne a makon da ya gabata bayan burin Tinubu na dawo da zaman lafiya da ɗorewar al’amura a shiyyar ya cika.

Saidai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a sa abinda shugaban ƙasar ya tattauna da Fubara a kai ba ko musabbabin zaman nasu.

Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan Tinubu ya gana da Shugaban ƙungiyar gwamnoni kuma Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRasaq; da Shugaban gwamnonin APC kuma Gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodimma; da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abass; da Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta ƙasa, FIRS, Zacch Adedeji; da Ministan Kuɗi, Wale Edun, da sauransu.

By Babaji