
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Gombe ta ce za ta fara gurfanar da iyaye da masu jiɓintar lamuran yara bisa rashin sanya su a makaranta.
Shugaban Hukumar Ilimi na Bai-ɗaya ta jihar (SUBEB), Babaji Babadidi ya faɗi haka a ranar Litinin, yayin ƙaddamar da shirin wayar da kan al’umma akan saka yara a makaranta a yankin Amada na Ƙaramar Hukumar Akko da ke jihar.
Ya ce, akwai yiwuwar iyayen da aka samu da aikata laifin su fuskanci zuwa gidan yari na watanni biyu ƙarƙashin sashe na 19(2) na dokar SUBEB gyarar 2021.
Babadidi ya bayyana cewa, an ɗauki matakin ne sakamakon nazari akan muhimmanci tabbatar da kowane yaro yana da ƴancin samun ilimi mai nagarta musamman a mataki na ƙasa, wato tun daga firamare zuwa sakandare (ƙarama da babba).
“Duk uba da ya saɓa wa sashe na 19(2) na kundin dokar, ya aikata laifi, kuma ya ɗauki alhaki, dokar haka zai biya tara ko kuma ya je kurkuku na wata ɗaya”, haka kuma idan mutun ya maimaita, za a sake cin sa tara ko shiga magarƙama na wata biyu.
Da fari, Shugaban na SUBEB ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin bai wa yara ilimi a kyauta, wanda ke harin yara guda 400,000, inda rashin samun haka zai sa a ƙaddamar da dokar.
A baya ne Kwamishinar Ilimi ta jihar, Farfesa Aishatu Maigari ta ce jihar tana da aƙalla yara 700,000 da ba sa zuwa makaranta.
