NRC ta gano gudu sama da kima da kuren ɗan-adam ne sababin gocewar jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da Tashoshin Jiragen ƙasa NRC, ta ce kuren ɗan-adam, gudu sama da kima da rashin aiwatar da tsarin agajin gaggawa a lokacin da ya dace sune dalilan gocewar jirgin Abuja zuwa Kaduna.

A ranar 26 ga watan Agusta, 2025 al’amarin ya auku jim-kaɗan bayan tashin jirgin daga Abuja, lamarin da ya raunata fasinjoji 22 da jefa ɗaruruwa cikin firgici.

Darakta-Manaja na NRC Dakta Kayode Opeifa ya sanar da haka a wata takarda ranar Litinin, bayan kammala bincike akan al’amarin.

Shaidu sun bayyana hatsarin a matsayin abin firgici da ban tsoro musamman bisa la’akari da harin ƴan bindiga na 2022 a lokacin da wani jirgi ya yi jigilar fasinjoji daga Abuj zuwa Kaduna, inda fasinjoji da dama suka rasu yayin da aka yi garkuwa da wasu.

A cewar Opeifa, al’amarin bai da alaƙa da zagon-ƙasa, saidai ya samu ne sakamakon tsaiko a wajen gudanarwa.

Ya ƙara da cewa, tuni hukumar ta fara ɗaukar matakan da suka dace wajen ganin ba a sake samun irin haka ba a nan gaba.

By Babaji