Da Ɗumi-Ɗumi: Ousmane Dembele na PSG ya lashe Ballon d’Or ta 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar Paris Saint Germain ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025.

An gudanar da taron ne a yau Litinin, 22 ga Satumba a ɗakin taro na “the Theatre du Chatelet’ a Paris.

Dembele ya doke matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal da takwaransa na ƙungiyar, wato Raphinha, kamar yadda ya sha gaban abokansa na PSG, Vitinha da Achraf Hakimi.

Ƙwallaye 35 ya ci wa PSG a kakar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadin ta lashe kofunan gida guda uku da na gasar zakarun Turai UEFA Champions League, da kuma zuwa wasan ƙarshe a FIFA Club World Cup.

By Babaji