Ba za a sake bada biza ga gurɓatattun ƴan Nijeriya da iyalansu ba, inji Gwamnatin Amurka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Amurka ta fitar da sabon gargaɗi ga gurɓatattun mutane ciki har da wasu manya a Nijeriya da ka iya fuskantar takunkumin samun bizar shiga ƙasar, a wani yunƙuri na yaƙi da rashawa a mataki na duniya.

Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya a wani shirin wayar da kan al’umma ta #VisaWise TravelSmart, ya ce an ɗauki matakin ne da nufin taimaka wa kauce wa shiga ayyukan rashawa da tabbatar da gaskiya da adalci akan waɗanda suka ci amanar shugabanci da dokar ƙasa.

Ƙasar ta kuma ce dokar ba akan iya masu irin laifin kaɗai ta tsaya ba, har ma da iyalansu.

A cewar ofishin, takunkumin bada bizar yana kan waɗanda aka samu da aikata laifuka kamar haka; cin hanci, damfara, ɓarnatar da dukiyar ƙasa, satar dukiyar al’umma, safarar haramtattun ababe da ayyukan da suka saɓa wa mulkin dimukraɗiyya.

Jami’ai sun bayyana cewa, matakin zai yi aiki ne a yayin da aka gaza yin shari’a akan irin haka, saboda haka sai a tabbatar da shi akan dukkan wanda lamarin ya shafa.

Haka kuma, sanarwar ta ce a ƴan shekarun nan ne aka sanya wa manyan ƴan kasuwar da ke safarar haramtattun sinadaran kayan maye da ƴan ƙasashen waje da ake zargi da tsoma baki a harkokin dimukraɗiyya a wasu sassan duniya takunkumin shiga Amurka.

By Babaji