
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 80, wanda zai gudana daga ranar Litinin zuwa 28 ga watan Satumba.
An tarbe shi a filin jirgin sama na John F. Kennedy, inda ya samu rakiyar ministoci da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, da Ministan Tsaro, Badaru Abubakar.
Shettima, wanda yake wakiltar Shugaba Bola Tinubu, zai gabatar da jawabi a madadin Nijeriya a taron, tare da halartar muhawarorin manyan shugabanni da kuma wasu tarurruka a gefen taron Majalisar.
Haka kuma, zai sanar da sabbin kudirin Nijeriya na rage dumamar yanayi (NDCs) ƙarƙashin yarjejeniyar Paris, tare da shiga tattaunawa kan samar da gidaje masu araha, tsaro da zaman lafiya, da kuma wasu muhimman yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashe.
Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya na ɗaukar nauyin jagorancin ƙoƙarin kafa dokar Majalisar Ɗinkin Duniya kan haraji, tare da matsa lamba kan batun sake fasalin kwamitin tsaro na MƊD domin ba wa Afirka aƙalla kujeru biyu na dindindin.
A cewarsa, wannan zai tabbatar da cewa muryar Afirka ta karaɗe duniya, yayin da Nijeriya kuma ke amfani da damar wajen jawo hannun jari a bangarorin ma’adinai, noma, fasaha da sauran manyan sassa na tattalin arziƙi.



