Babaji

5698 Posts

‘Yan adawa sun jingine ADA, sun zaɓi ADC yayin da Pantami, El-Rufa’i da wasu suka haɗe da Atiku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɓangaren haɗakar ƴan adawa da ke neman karawa da Shugaba Bola Tinubu da jam'iyya mai mulki ta APC a zaɓen 2027, ya zaɓi jam'iyyar ADC a hukumance a matsayin wadda za ta jagoranci fitar da ƴan takararsa sauransu al'amuransu na siyasa Hakan na nufin ta jingine batun shirin neman yi wa sabuwar jam'iyya mai suna ADA rajista. An cimma matsayar haka ne yayin da masu ruwa da tsaki suka gudanar da wani zama a Abuja ranar Alhamis, wanda ya samu halartar jiga-jigan ƴan siyasa daga sassan ƙasar daban-daban. Tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta haramta karɓar kuɗaɗe ba bisa doka ba a kwalejojin fasaha

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta nanata cewa baki ɗaya kwalejojin fasaha da ke faɗin Nijeriya tana ɗaukar nauyin dukkan abinda ya shafi dawainiyarsu, inda ta gargaɗi jagororinsu da su kauce wa ƙaƙaba wa ɗalibai kuɗaɗen lamuran karatunsu ba bisa ƙa'ida ba. A sanarwar da Daraktan yaɗa labarai ta Karamin Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, wato Folasade Boriowo ta fitar, Ministan ya ce karatun makarantun na FTCs kyauta ne, kamar yadda gwamnati ke ɗaukar nauyin baki ɗaya kashe-kashen da ake yi acikinsu. A cewarsa, gwamnati tana biyan dukkan buƙatun ɗalibai da suka haɗa da wuraren kwana, inifom,…
Read More

Atiku ya ƙaryata alƙawarin bogi ga Yarabawa da nesanta kansa daga wanda ya yaɗa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya nesanta kansa daga kalaman da aka jingina masa na soki burutsu da wani mai suna Kola Johnson da ya yi bayan ikirarin shi mai taimaka masa ne akan harkokin yaɗa labarai. A cikin saƙon, wanda aka baza wa duniya a ranar Laraba, an ce wai Atiku ya yi alƙawarin fifita buƙatun Yarabawa idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa a zaɓen 2027. Haka kuma, saƙon ya ƙunshi cewa gwamnatin Atiku za ta fifita wata ƙabila…
Read More

Kano: Ya yi ajalin kakanninsa kan rikicin abinci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Alhamis aka samu labarin wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Mutawakkilu Ibrahim a jihar Kano, wanda aka zarge shi da laifin halaka kakansa da kakarsa a sakamakon rikici akan abinci. Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya faru ne a yankin rukunin gidaje na Ƙofar Dawanau da misalin ƙarfe 9:30 na safe, wanda ya jefa al'umma cikin firgici da alhini. A wata takarda daga Kakakin Rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, Muhammad Ɗansokoto mai shekaru 75 da Hadiza Tasidi sune waɗanda aka halaka yayin harin a gidansu. SP Kiyawa ya…
Read More

Sufeto Janar na ƴan sanda ya bada cakin biliyan N2 ga iyalan jami’an da suka rasu a bakin aiki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sufeto-Janar na ƴan sanda (IGP), Kayode Egbetokun ya miƙa caki ga iyalai guda 1,574 a ƙarƙashin Shirye-shiryen Insorar rai da Walwalar Iyalai na IGP, waɗanda aka rasa daga shekarar 2015 zuwa 2025 ciki har da wasu haƙƙoƙinsu na tsawon shekaru goma. Blueprint ta ruwaito cewa, Rundunar ƴan sanda ƙarƙashin Sufeto-Janar Egbetokun ta biya kimamin Naira biliyan 24.2 ga iyalai 9,735 na jami'an da suka rasu a bakin aiki a faɗin Nijeriya. Da yake magana yayin gabatar da cakin ga iyalan jami'an a Abuja ranar Laraba, Shugaban ƴan sandan ya yi alhini da jajenta wa…
Read More

Gwamnatin Sakkwato ta dakatar da karɓar kuɗin karatu a sakandare

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni daga Jihar Sakkwato sun bayyana cewa, Kwamishinan Ilimi, Farfesa Ladan Ala ya umarci jagororin makaratun sakandare na gwamnati da ke jihar da su dakatar da karɓar kuɗin karatu daga iyayen yara. Hakan ya biyo naɗa kwamiti da Ma'aikatar Ilimi ta jihar yi domin yin nazari game da ƙorafe-ƙorafen da al'umma ke yi a jihar na kuɗaɗen karatu da ake karɓa a makarantu. A cewar Kwamishinan, an dakatar da haka ne har zuwa lokacin da kwamitin zai bada rahotonsa akan matakan da suka dace a ɗauka akan lamarin. A wata takarda daga jami'in yaɗa…
Read More

An ga shugaban EFCC yayin da Tinubu ya gayyaci tsohon kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yammacin jiya Laraba Shugaba Bola Tinubu ya gayyaci Kantoman Jihar Ribas, VA Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), zuwa Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa, Ibas, wanda ya bar ofis a ranar 17 ga watan Satumba, 2025 bayan kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci a jihar, ya isa Fadar ne da misalin ƙarfe 6:50, inda wasu jami'ai suka tarbe shi tare da masa iso zuwa wajen shugaban ƙasar. A tare da shi an ga Ministan Kuɗi, Wale Edun da Shugaban Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) Ola Olukoyede, waɗanda ke bada…
Read More

Filato: Ɗan majalisar da aka yi garkuwa da shi ya samu shaƙi iskar ƴanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƴan uwa da abokan arziƙi sun samu numfasawa bayan da ɗan majalisar dokokin Filato da ke wakiltar Pankshin ta Kudu, Laven Denty Jacob ya kuɓuta daga hannun ƴan bindiga kwanaki kaɗan da yin garkuwa da shi a jihar. Da yake tabbatar da lamarin a ranar Laraba, Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Hon. Kwarpo Sylvanus, ya ce Hon. Jacob ya samu komawa wajen iyalansa cikin ƙoshin lafiya. Ya bayyana cewa, an sako shi ne a daren Talata wayewar Laraba ya bayan ya bar hannun ƴan bindigar, saidai ba su da masaniyar ko an biya…
Read More

Rikita-rikita: Remi Tinubu ta sanya sunan Marigayi Buhari cikin waɗanda suka tallafa mata tara biliyan N20

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma sun fara cecekuce a yayin da matar Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta sanya sunan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari acikin jaddawalin waɗanda suka tallafa mata wajen tara biliyan N20 domin kammala gina ɗakin karatu na ƙasa a Abuja. A ranar 1 ga watan Satumba matar shugaban ƙasar ta shelanta sadaukar da bikin cikar ta shekaru 65 wanda da za a yi a ranar 21 ga watan, ga kammala gina ɗakin karatu na ƙasa da aka ɗauki tsawon lokaci da farawa. Akan haka ne ta roƙi abokai, masoya da ɗaukacin al'ummar Nijeriya…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: An naɗa Sheikh Saleh bin Humaid a matsayin sabon babban mai fatawa na Saudiyya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Masarautar Saudiyya ta naɗa Sheikh Dakta Saleh bin Humaid a matsayin sabon mai fatawa na ƙasar kuma shugaban babbar majalisar manyan malamai. Sarki Salman ya naɗa Sheikh Humaid a muƙamin kwana ɗaya da rasuwar Sheikh Abdulaziz bin Abdullah al-Sheik, kamar yadda jaridar Inside the Harmain ta wallafa a yau Laraba. A jiya Talata Sheikh Abdullah al-sheik ya rasu yana da sama da shekaru 80 a duniya bayan shafe sama da shekaru 25 a muƙamin. A shekarar 1949 aka haifi Sheikh Humaid, wanda ɗaya ne daga cikin limamai tara na babban masallacin Makkah. Haka kuma…
Read More