27
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an tsaro na haɗaka (CJTF) reshen Arewa ta Gabas da ke aiki ƙarƙashin atisayen Haɗin Kai, sun yi nasarar daƙile ayyukan jigilar wasu kayan aiki ga mayaƙan Boko Haram da na ISWAP tare da kama wasu da ake zargi akan haka a jihohin Borno da Adamawa. A tsakanin ranakun 19 da 24 ga Satumba, 2025 sojojin Operation Desert Sanity IV suka ƙwato wani adadi na fetur da taki da aka yi fasa-ƙaurin su. A yayin haka ne suka halaka ɗan leƙen asirin ƴan ta'adda da kama wasu mutane biyu da ke yi wa mayaƙan…
