
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon gwamnan Jihar Oyo, Oba Rashidi Ladoja ya zama sarki na 44 a Masarautar Ibadan, wato 44th Olubadan of Ibadanland.
A yau Juma’a, 26 ga Satumba aka naɗa Ladoja a wajen bauta na Ose Meji da ke Ƙaramar Hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas a jihar.
A ɗakin taro na Mapo Hall ne za a bai wa sabon sarkin sandar mulki a yayin gabatar da shi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde na jihar.
Ladoja ya samu muƙamin ne sakamakon rasuwar sarkin masarautar na 43 a watan Yuli, 2025, wato marigayi Oba Owolabi Olakunlehin.
