Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya je Ibadan karo na farko a matsayin shugaban ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Bola Tinubu ya bar Abuja domin zuwa Ibadan, Babban Birnin jihar Oyo, inda zai halarci naɗin sarautar sabon Sarkin Masarautar Ibadan, Rashidi Ladoja.

Shugaban ƙasar ya bar Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 12:45 na rana a yau Juma’a.

A birnin Ibadan ne Tinubu zai jagoranci sauran manyan ƙasa zuwa wajen naɗin sarautar sabon sarkin a ɗakin taro na Mapo mai daɗaɗɗen tarihi.

Tsohon gwamnan na Oyo ya zaman sarkin Masarautar ne na 44 bayan rasuwar Oba Owolabi Olakulehin a ranar 7 ga watan Yuli, 2025.

Wannan shi ne karo na farko da Shugaba Tinubu ya ziyarci Ibadan tun zuwansa a watan Fabarairun 2023.

By Babaji