28
Sep
Rikici tsakanin Ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN da Matatar Ɗangote ya ƙazanta, lamarin da ya sa ƙungiyar ta bada umarni ga mambobinta da su tsunduma a yajin aiki a faɗin ƙasar. Hakan zuwa ne kwanaki kaɗan da sallamar ma'aikata sama da 800 da ƙungiyar ta zargi Matatar ta Dangote a kai. PENGASSAN ta bayyana cewa korar ɗimbin ma’aikata a kamfanin ba bisa ka’ida ba ne, wanda ya saba wa haƙƙin ƙwadago kuma ka iya zama babbar barazana a nan gaba. A wata sanarwa, ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa kamfanin ya maye gurbin ma'aikatan da aka kora da Indiyawa…
