29
Sep
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Haɗakar malaman Ahlussunnah Wal-Jama'ah ta Kano ta yi tir da kalaman Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo cewa hukuncin da aka yanke wa Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara kan ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) abu ne da aka siyasantar da shi. A wata takarda da ta fitar ta hannun Farfesa Muhammad Muslim Ibrahim, tawagar malaman ta ce furucin nasa abu ne da zai iya jefa al'umma cikin ruɗani duba da cewa kotu ta riga ta yanke masa hukunci. A jiya Lahadi, 28 ga watan nan na Satumba, 2025, Mataimakin gwamnan ya yi tsokaci akan lamarin…
