Babaji

5698 Posts

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da kwamishinan zaɓe na Neja, tsohon shugaban SUBEB da ɗimbin matafiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan bindiga sun yi garkuwa da Ahmed Mohammed, da aka fi sani da Barista Ahmed Lauya, wanda kuma shi ne kwamishinan zaɓe na hukumar zaɓe ta jihar Neja da direbansa da tsohon Shugaban SUBEB Mohammed Bawa Niworu da kuma wasu matafiya ta dama. Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya auku ne a safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Satumba a titin Zugurma zuwa Ibbi zuwa New Bussa kusa da filin shaƙatawa na ƙasa da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu. Wata majiya ta ce al'amarin ya faru ne a lokacin da mutanen ke kan hanyarsu ta…
Read More

Tinubu ya umarci a yi bincike akan kisan ƴar jaridar Arise News

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya koka game da kisan Somtochukwu Christelle Maduagwu, wadda ƴar jarida ce a gidan talabijin na Arise, a yayin wani fashi da ɓarayi suka ƙaddamar a gidanta da ke Katampe a Abuja a daren ranar Lahadi wayewar Litinin. A wata takarda daga Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya bayyana ƴar jaridar a matsayin ƙwararriya a fannin aikinta wadda ta rayu na gajeren zango bisa iftila'in da ya same ta. Don haka ya umarci hukumomin tsaro da su ƙaddamar da bincike akan kisan nata, yana mai alwashin sai an hukunta…
Read More

Kano: Ƙungiyar ƴan kasuwa ta kai wa jagorori da malamai ziyara a Bichi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar 'Yan Kasuwar Karamar Hukumar Bichi ts 'Bichi Traders Multi-purpose Cooperative Society Limited' ta kai ziyarar ban girma da neman shawarwari ga manyan shugabanni da malamai a garin Bichi da nufin bunƙasar harkokin kasuwanci da inganta tattalin arziƙin ƙaramar hukumar. A sanarwar da Jami'ar Yada Labarai ta Karamar Hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, ta ce da fari ƙungiyar ta kai wa Farfesa Arma Ya’u Hamisu Bichi ziyara wanda shugaba ne kuma jagoran al’umma, inda ya yi addu’a da fatan alkhairi ga kungiyar tare da bayyana farin ciki da jin daɗinsa a kan…
Read More

Ni yanzu ba ɗan siyasa ba ne, inji sabon Sarkin Masarautar Yarabawa, Ladoja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sarkin Masarautar Ibadan na 44, Oba Rashidi Adewolu Ladoja, wato Arusa na I, ya sanar da yin murabus daga harkokin siyasa bayan rantsar da shi a matsayin sarki. Sarkin, wanda tsohon gwamnan Jihar Oyo ne, ya faɗi haka ne a jiya Talata yayin da ya karɓi baƙoncin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i da tsohon shugaban Majalisar Dattawa Iyorchia Ayu da wasu masu alfarma a Fadarsa da ke Ibadan. Oba Ladoja ya ce, ya yanke hukuncin ne saboda sabon muƙamin da ya samu na zama sarkin. Ya kuma…
Read More

Jawabin ranar ƴancin kai: Tinubu ya jinjina wa ƴan mazan jiya da lissafo nasarorin da gwamnatinsa ta samu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yayin jawabinsa na ƙasa a safiyar yau Laraba da Nijeriya ke cika shekaru 65 da samun ƴancin kai, Shugaba Bola Tinubu ya yi jinjina ga ƴan mazan jiya da kuma zayyano wasu nasarori da aka samu a ƙarƙashin gwamnatinsa. Tinubu, wanda wannan shi ne karo na uku da yake gabatar da jawabin ƴancin kai a matsayin shugaban ƙasa, ya ce wannan lokaci ne na nazarin muhimman al'amuran ƙasa da sabunta fata. Ya yaba wa sadaukarwar da ƴan mazan jiya suka yi wa ƙasar kamar su Nnamdi Azikiwe, Obafemi Awolowo, Ahmadu Bello, Tafawa Ɓalewa,…
Read More

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta tallafa wa Gidauniyar Malala da inganta ilimin ƴaƴa mata

Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya ta jaddada kudirinta na yin aiki tare da wata kungiyar rajin ilimin ‘yaya mata, mai suna Malala Fund a kokarinta na magance kalubalen da ke hana miliyoyin yara, musamman ‘yan mata rashin zuwa makaranta. A yayin wani taro da aka gudanar a Abuja tare da mai lambar yabo ta Nobel Laureate da Malala Fund, Ms. Malala Yousafzai, tare da tawagar kungiyar, mai kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mr. Mohamed Malick Fall, ya jaddada sadaukarwar Majalisar Dinkin Duniya na bunkasa ilimi mai hade da daidaito ga kowa. "Majalisar Dinkin Duniya…
Read More

Kotu ta umarci Sufeto Janar ya kama Shugaban INEC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Osogbo, babban birnin jihar Osun, ta umarci Sufeto Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun da ya kama Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu bisa nuna raini ga kotu da ƙin biyayya ga dokokin ƙasa. Mai shari'a, Funmilola Demi-Ajayi ta bayyana haka a ranar Litinin bayan jam'iyyar AA (Action Alliance) ta shigar da ƙara akan INEC. Alƙalin ta ce, da Farfesa Yakubu da hukumar zaɓen sun yi buris da hukuncin da aka yi da fari na tabbatar da shugabannin jam'iyyar na jihohi ƙarƙashin jagorancin Adekunle…
Read More

2027: Gwamnatin Tarayya ta magantu kan tsayawa takarar Jonathan, ta zarge shi da almubazzarantar da Dala biliyan 66

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta yi tsokaci game da rahotannin da ke cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ka iya tsayawa takara a zaɓen 2027, tana mai gargaɗin cewa ƴan Nijeriya ba za su manta da abinda da ta kira da tarihin ƙuncinsa a karagar mulki ba. Kakakin shugaban ƙasa Bayo Onanuga a wata takarda, ya ce bayyana haka bayan da tsohon ɗan siyasa, Jerry Gana ya ce akwai yiwuwar Jonathan ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa a babbar jam'iyyar adawa ta PDP. A cewar Gana, Jonathan ka iya kayar da Shugaba Bola Tinubu…
Read More

‘Yan fashi sun halaka ƴar jaridar Arise News, Sommie a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar gudanarwa da ma'aikatan gidan talabijin na ARISE News na jimamin rasuwar ɗaya daga cikin jami'ansu mai haskawa, wato Somtochukwu Christelle Maduagwu. Ta rasa ranta ne a hannun ƴan fashi a gidanta da ke Katampe a Abuja, a lokacin da suke je fashi a yankin. Rahotanni sun bayyana cewa iftila'in ya auku ne a safiyar ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025, wanda a yanzu Hukumar ƴan sandan take bincike a kai. Somtochukwu da aka fi sani da Sommie, an haife ta ne a ranar 26 ga watan Disambar 1995, ma'ana a matsayinta na ƴar…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta soke faretin ranar ƴancin kai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke faretin da ta shirya da farko domin bikin cikar shekera 65 da samun ƴancin kan Nijeriya a ranar 1 ga watan Oktoba. Daraktan yaɗa labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), Segun Imohiosen ya faɗi haka a wata takarda. A cewar saƙon da ke ciki, gwamnatin ta bada haƙuri akan takura da hakan ka iya haifar wa al'umma. Imohiosen ya bayyana cewa, hakan bai ragi muhimmanci ko darajar ranar ba, sannan gwamnatin tana aiki tuƙuru wajen ganin ta an yi bikin cikin walwala. Za kuma a gudanar da…
Read More