03
Oct
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon sanatan da ke wakiltar Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo ya miƙa kansa ga Hukumar ƴan sanda ɓangaren binciken manyan laifuka (FCID) a Abuja bayan an zarge shi da yi wa ɗalibar makarantar sakandare mai shekaru 13 fyaɗe. Blueprint ta ruwaito cewa ana kan aiki akan batun duk da cewa wasu sanannun ƴan Adamawa sun yi ƙoƙarin sanyaya gwiwar iyayen yarinyar don su janye daga ƙorafi a kai. Wakilin jaridar ya ruwaito cewa iyayen sum shaida wa ƴan jarida cewa tsohon sanatan kuma ɗan takarar gwamna, ya sha ziyarar gidan su yarinyar domin roƙon…
