04
Oct
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban jagoran al'ummar Kirista na Jihar Sakkwato Matthew Hassan Kukah ya bayyana cewa ina ma ace Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya fifita ɗorewar al'amura da haɗin kan al'umma a zamanin mulkinsa sama da yaƙi da rashawa a ƙasar da ke a rarrabe. Ya ce, yaƙi da rashawa abu ne da ke da muhimmanci wajen ciyar da ƙasar gaba, amma haɗin kan al'umma da ɗorewar al'amura su suka fi muhimmanci. Babban faston ya kuma ce, akwai buƙatar Gwamnatin Tarayya ta ƙara himma wajen kawo ƙarshen ta'addanci a Nijeriya da warware matsalar ƙoƙarin ɓalle wa daga…
