05
Oct
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce jimillar jami'an sojoji 16 ne za a yi wa hukunci bisa zargin su da laifukan rashin biyayya da karya wasu dokokin aiki. Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya bayyana haka a wata takarda, ranar Asabar. Ya ce, an kama jami'an ne a yayin wani atisaye na musamman bayan gudanar da bincike akan wasu ayyuka da suka ci karo da ladabtarwar sojoji da ƙwarewar aiki. A cewarsa, sakamakon bincike ya nuna cewa wasu daga cikin jami'an an same su ne da laifukan sakamakon ƙunci da…
