
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Cocin ƙasar Ingila ya naɗa Sarah Mullally a matsayin sabuwar jagora ta Canterbury, lamarin da ya yi silar zaman ta mace ta farko da ta taɓa samu muƙamin a tsawon tarihin kusan shekaru 500 na cocin.
Sarki Charles ya tabbatar da naɗin Mullally mai shekaru 63, wanda tuni ya fara aiki a ranar 3 ga watan Oktoba.
Don haka daga yanzu ta zama jagorar mabiya ɗariƙar Anglican na faɗin duniya, waɗanda adadinsu ya kai kusan miliyan 85.
Da fari ita ce babbar fastowa mai daraja ta uku a cocin tun a 2018.
An naɗa ta ne shekara guda da Justin Welby ya yi murabus daga muƙamin sakamakon suka da yake sha kan salon hukuncinsa na cin zarafin yara.
