Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ko’odinetan ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta ƙasa (HURIWA), Kwamared Emmanuel Nnadozie Onwubiko, a ranar Talata, ya bayyana sakacin ma’aikatan babban asibitin Maitama Abuja a matsayin abin da ya taimaka wajen mutuwar ’yar jarida gidan talbijin na Arise, Somtochukwu Christelle Maduagwu.
Tashar talabijin ta ARISE News ta sanar da rasuwar ma’aikaciyarta, Somtochukwu Christelle Maduagwu, wacce aka kashe a safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Satumba, 2025 sakamakon wani harin fashi da makami da aka kai a gidanta da ke unguwar Katampe a Abuja.
A cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, Onwubiko ya ce, dagewar da asibitin ya yi kan rahoton ‘yan sanda kafin a yi mata magani ya nuna ƙarara irin rashin sanin makamar aiki da ya mamaye tsarin kiwon lafiyar mu.
“Mutuwar mutane da yawa, kamar yadda rahotanni suka nuna, sun faru ne sakamakon rashin gabatar da rahoton ‘yan sanda da waɗanda abin ya shafa suka yi. Wannan tsari yana fifita dokar da ba ta wajabta fiye da lafiyar ɗan Adam, kuma tsari ne da ya kamata a canja shi.
“Ya kamata a tuhumi babban daraktan kula da lafiya na asibitin Maitama kuma a kori shi cikin gaggawa saboda rashin iya aiki da ya yi sanadiyyar rasuwar Somto.
“Bugu da ƙari kuma, muna nuna ɓacin ranmu kan yadda ‘yan sanda suka kasa bayar da taimako a lokacin da aka kira su da su kai Somto asibiti, wai saboda rashin man fetur, wannan wani haƙƙi ne da ba za a amince da shi ba, kuma ya kamata masu hannu da shuni su fuskanci sakamako.
“Gazawar ‘yan sanda wajen isa wuraren d ake fama da rikici cikin gaggawa ya nuna ƙarara cewa akwai buƙatar yin garambawul da sake fasalin ƙasa, muna kira ga IGP, Sufeto Janar Kayode Egbetokun da kuma buƙatar gwamnati ta zauki matakin gaggawa don magance waɗannan matsalolin da kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro sun samar da kayan aikin da za su iya mayar da martani mai inganci a cikin gaggawa,” inji shi.
