Jami’ar ABU ta yi addu’ar ci-gaba mai ɗorewa yayin cikarta shekeru 63 da kafuwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An gudanar da taron cika shekaru 63 da kafa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da addu’o’i na musamman a jiya Asabar, 4 ga watan Oktoba.

Daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Auwalu Umar ya faɗi haka a wata takarda ranar Asabar.

Ya ce, a ranar 4 ga watan Oktoba, 1962 aka kafa makarantar, inda a jiya ɗalibai da malamai a masallatai da coci da ke sashenta biyu suka gudanar da addu’o’in cigaba da samun nasara a gare ta.

An yi haka ne nufin neman taimakon ubangiji wajen ciyar da harkokinta gaba da bunƙasarsu.

A cewarsa, Mataimakin Shugaban jami’ar (VC) Farfesa Adamu Ahmed zai gabatar da taron manema labarai tare da bayyana gudumawar da jami’ar ta bayar ga ƙasa, shiyya da ma mataki na duniya.

Tun a shekarar 1959 ne aka fara nazarin samar da fagen karatu da za a riƙa horar da ɗalibai a fannonin ilimi daban-daban a matakin gaba da sakandare, lamarin da ya janyo kafa jami’ar a Zariya.

Akan haka aka kafa kwamitin doka na shirin kafa ta a watan Afrilun 1961 ƙarƙashin Majalisar Dokokin Arewa.

A ranar 4 ga watan Oktoba, 1962 aka kafa ta da sunan Sir Ahmadu Bello, wanda shi ne Sardaunan Sakkwato kuma Frimiyan Arewa, sannan kuma shugaban jami’ar ta ABU na farko.

By Babaji