NAFDAC ta rufe manyan shagunan ƴan Chana biyu a Abuja

Spread the love

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta rufe manyan shagunan ƴan Chana guda biyu da ke yankin Jabi a Abuja.

Haka kuma ta kulle wasu shagunan kayan shafe-shafe guda takwas a kasuwar Wuse saboda karya ƙa’idojin sayarwa, da rarrabawa da kuma rubuta sunayen kayayyaki.

A sanarwar da Mataimakin Daraktan hulɗa da jama’a na hukumar, Adegboyega Osiyemi, ya fitar ranar Juma’a, ya ce mataki ya biyo bayan umarnin Daraktar Hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ne inda tawagar NAFDAC ta ƙwace kayayyakin da ba su dace ba da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 170.

NAFDAC ta ce, an rufe shagunan da ke Mike Akhigbe Way da Ebitu Ukiwe Street bayan rahotanni daga masu amfani da kayayyaki da kuma bincike sun tabbatar da cewa shagunan na sayar da abinci da aka rubuta sunayensu da Sinanci kawai, ba tare da fassarar Turanci ba, lamarin da ya saɓa wa tsarin Nijeriya.

Sannan, jami’an NAFDAC sun gano cewa ɗaya daga cikin shagunan yana aiki da cikakken kayan da ba a yi musu rajista ba.

Kamar haka ne a kasuwar Wuse, aka rufe shagunan kayan shafe-shafe guda takwas da ake zargi da sayar da kayayyaki da aka haramta, waɗanda wa’adin su ya ƙare, da kuma waɗanda ba su da rajista.

Bincike ya gano cewa wasu ƴan kasuwa suna shiga irin ta likitocin fata da masu bayar da magani, suna rubuta kayayyaki masu haɗari ga mutane da nufin sanya fata fari, da gyaran jiki ko ƙara kuzarin jima’i.

Daga cikin kayan da aka ƙwace akwai magungunan sanya fata fari, da ƙwayoyin ƙara kuzari, da wasu magungunan gargajiya da kayan shafe-shafe da ake danganta su da haɗarin cutar da ƙoda, da fita daga hayyaci da ciwon daji na fata.

Farfesa Adeyeye ta jaddada ƙudirin hukumar na kare lafiyar ƴan Nijeriya, tare da shawartar al’umma da su riƙa amfani da kayayyaki da aka tabbatar da rajistarsu a hukumar.

By Babaji