07
Oct
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya kira taron gaggawa na majalisar ƙasa da majalisar ƴan sanda, wanda za a yi a ranar 9 ga watan nan na Oktoba, a wani mataki na ƙoƙarin warware matsalolin taɓarɓarewar harkokin tsaro. Za a gudanar da taron ne a zauren majalisar tattaunawa ta Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, wanda zai haɗa tsofaffin shugabannin ƙasa, gwamnoni, tsofaffin ministocin shari'a da wasu manyan jagororin tsaro. A cewar wata takarda daga Sakataren harkokin manyan jami'an gwamnati ƙarƙashin kulawar Sakataren Gwamnati (SGF), Sanata George Akume, tuni aka aika da saƙonnin gayyata ga mambobin…
