
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Talata Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ke shirin komawa bakin aiki bayan ɗauki-ba-daɗi na tsawon watanni shida sakamakon dakatar da ita da aka yi daga harkokin Majalisar Dattawa.
Hakan na zuwa ne yayin da ƴaƴan Majalisar Dattawan ke komawa aiki bayan hutun watanni biyu.
Lauyan Natasha, Barista Victor Giwa ya tabbatar da haka a wata hira da manema labarai, inda ya ce za ta koma a matsayin sanata bayan kammala dakatarwar wata shidan da aka yi mata.
Da fari majalisar ta ɗage komawarta aiki daga 23 ga watan Satumba zuwa 7 ga watan Oktoba, wanda ya faru ne sakamakon muhimman batutuwan ƙasa da suka haɗa da gyaran kundin dokar ƙasa da ƙudirorin gyare-gyaren tattali.
Masu sharhi akan harkokin siyasa na zuba ido akan ko za a bar Sanatar ta koma aiki ba tare da wani tsaiko ba, duk cewa lauyan nata ya ce ta kammala wa’adin dakatarwar da aka ɗiba mata.
A cewarsa, yunƙurin dakatar da ita daga komawa, abu ne da ya saɓa wa hukuncin da doka ta tanada.
