Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Ƙungiyar jin ƙai ta dangin juna Afrika Initiative (DJAI) ta gudanar da rabon kayan abinci ga mutane 120 masu rauni da marasa ƙarfi a masarautun Fika da Potiskum da ke Jihar Yobe. A wani ɓangare na shirin ta na shekara-shekara na taimako.
Da yake jawabi a fadar mai martaba sarkin Fika da ta Mai Potiskum, shugaban ƙungiyar na ƙasa, QS Usman BK, ya ce shirin na cikin ƙoƙarin rage wa marasa galihu raɗaɗin rayuwa da kuma ƙarfafa halin sadaka da taimako a tsakanin membobin ƙungiyar.
Ya bayyana cewa membobin ƙungiyar na tara kuɗi a duk wata domin gudanar da wannan aiki, sannan su ƙara bayar da gudunmawa lokacin da ake shirin gudanar da rabon kayan.
Ya kuma gode wa sarakunan Fika da Potiskum bisa karɓar tawagar da kuma goyon bayan da suke ba ƙungiyar wajen ayyukan jin ƙai.
Mai Fika, wanda Chokalin Fika, Alhaji Abubakar Muhammad, ya wakilta, ya yaba wa ƙungiyar bisa wannan aiki na alheri, yana mai cewa taimakon ya zo a lokacin da mutane ke fama da matsin tattalin arziki.
Haka zalika, Mai Potiskum, Mai Martaba Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya jinjinawa ƙungiyar bisa wannan ƙoƙari, tare da shawartar masu amfana da su yi amfani da kayan yadda ya kamata ba tare da sayar da su ba.
Shugaban ƙungiyar, QS Usman BK, ya ƙara bayyana cewa wannan rabon abinci ya zo ne a yayin bikin cika shekara goma da kafa ƙungiyar, inda kowace shekara ake zaɓar wata jiha domin karɓar baƙuncin shirin a matakin ƙasa.
Kayan da aka raba sun haɗa da buhunan shinkafa masu nauyin kilo 7, taliya (spaghetti), da ɗan kuɗin taimako ga wasu daga cikin masu amfana.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana sun gode wa ƙungiyar Dangin Juna Afrika Initiative bisa wannan taimako, tare da yin addu’a ga Allah (SWT) ya saka musu da alheri.
