Tinubu ya gayyaci tsofaffin shugabanni da ƴan sanda kan taɓarɓarewar tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya kira taron gaggawa na majalisar ƙasa da majalisar ƴan sanda, wanda za a yi a ranar 9 ga watan nan na Oktoba, a wani mataki na ƙoƙarin warware matsalolin taɓarɓarewar harkokin tsaro.

Za a gudanar da taron ne a zauren majalisar tattaunawa ta Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, wanda zai haɗa tsofaffin shugabannin ƙasa, gwamnoni, tsofaffin ministocin shari’a da wasu manyan jagororin tsaro.

A cewar wata takarda daga Sakataren harkokin manyan jami’an gwamnati ƙarƙashin kulawar Sakataren Gwamnati (SGF), Sanata George Akume, tuni aka aika da saƙonnin gayyata ga mambobin majalisun na su halarta kai-tsaye ko kuma ta hanyar wakilci.

Ya ce, zaman zai mayar da hankali ne akan al’amuran tsaron ƙasa da harkar ƴan sandan, wanda za a fara da misalin ƙarfe 1 na rana, wato na majalisar tsofaffin shugabannin ƙasa, sai kuma na ƴan sanda da misalin ƙarfe 2 na rana.

Majiyoyi daga Fadar sun shaida wa manema labarai cewa zaman zai mayar da hankali ne wajen tattauna batutuwan ayyukan sojoji da ƴan sanda wajen magance matsalolin ta’addanci da garkuwa da mutane da faɗan ƙabilanci musamman a yankunan Arewa ta Yamma da ta Tsakiya da kuma Birnin Tarayya Abuja.

Haka kuma, akwai batutuwan gyare-gyare a harkar ƴan sanda da samar da ƴan sandan yankuna da kuma naɗa magajin shugaban hukumar zaɓe, wanda wa’adinsa zai ƙare nan da ƙarshen shekarar nan.

By Babaji