Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya umarci hukumar alhazai ta rage kuɗin aikin hajjin 2026

Spread the love

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) da ta rage kudin aikin hajji na shekarar 2026 domin saukaka wa ‘yan Najeriya.

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ya bukaci a sake fasalin tsarin hada-hadar aikin hajji domin ya kasance cikin sauki, ga masu ƙaramin karfi da ke da burin sauke farali.

Matakin ya biyo bayan koke-koken da al’umma suka yi game da tsadar aikin hajjin bana.

Tinubu ya ce gwamnati za ta tallafa wa NAHCON da duk abin da ya dace don ganin an samu tsari mai kyau da araha, tare da tabbatar da inganci da jin dadin mahajjata.

Hukumar NAHCON na sa ran fitar da cikakken sabon tsari nan ba da jimawa ba.

By Babaji