‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Taron an shirya shi ne akan faɗakar da masu sana’ar gwangwan kan hatsarin ɗaukar ababen fashewa a Katsina.
‘Yan sandan sun gabatar da wasu daga cikin ababen fashewa dake barazana da rayuwar al’umma a yayin taron.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina tare da haɗin gwiwar Kamfanin NAK Steel Rolling Processing Mill Limited da Ƙungiyar Masu Sana’ar gwangwani na Najeriya (NASWDEN) suka shirya wani taron wayar da kai da faɗakarwa ga masu sana’ar gwangwani da sauran masu sana’ar ƙarafa.
Da yake jawabi a lokacin taron, mai magana da yawun ‘yan sanda na Jihar Katsina PPRO Abubakar Sadiq ya bayyana manufar wannan taro a matsayin hanyar sanar da mahalarta game da hatsarin da ke tattare da abubuwan fashewa da ake iya samun su a cikin tarkacen ƙarafa, da kuma hanyoyin guje wa faɗawa cikin haɗari.
Haka zalika CSP Bushmang Emmanuel tare da Eng. Tukur Lawal sun yi nuni da cewa wasu daga cikin abubuwan fashewar da aka bari a wuraren da aka yi amfani da su a baya na iya shiga cikin gwangwani ko ƙarafa, abin da ka iya janyo mummunan bala’i idan aka yi mu’amala da su musamman idan suka haɗu da wasu ƙarafa.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina wanda ya samu wakilcin ACP Suleiman Nasir Ringim ya bayyana wannan taron faɗakarwa a matsayain abun da zai taimaka matuƙa wajen rage haɗarin fashewar abubuwa a cikin al’umma, musamman ma ga masu sana’ar tattara shara da ƙarafa.
Ya kuma yi kira ga dukkan masu sana’ar su riƙa lura sosai, tare da gaggauta sanar da hukumomi idan sun ci karo da wani abu da suka zaci abin fashewa ne.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar masu sana’ar gwangwani ya gode wa rundunar ‘yan sanda da sauran abokan haɗin gwiwa bisa wannan muhimmiyar gudummawa, inda ya ce hakan zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, da kuma inganta tsaro a fannin sana’arsu.
baki ɗaya.
Ya’yan ƙungiyar da suka fito daga ƙananan hukumomi 34 suka halarci taron.
