Takardun bogi: Ministan Kimiyya ka iya murabus yayin da Jami’ar UNN ta musanta yaye shi a matsayin ɗalibinta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Cif Uche Geoffrey Nnaji ya shiga halin tsaka mai wuya bayan da kotu ta ayyana cewa Jami’ar Nsukka (UNN) da ya yi ikirarin yin karatu acikinta ba ta ba shi takardar kammala karatun digiri ba.

Wani rahoto da jaridar premium Timesta wallafa ya ce an gano cews ministan ya miƙa takardun bogin ga Majalisar Dattawa domin tattance shi, bayan shugaban Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunansa cikin waɗanda yake so ya ba muƙamin minista a shekarar 2023.

Ta yi ikirarin cewa takardun shaidar kammala karatun digiri da na bautar ƙasa na Nnaji duka na bogi ne.

Inda ta ƙara da cewa, masu suka sun ce Ministan bai kammala karatun digirin ba, sannan takardar shaidar bautar ƙasar da ya bai wa ofishin sakataran gwamnatin tarayya da hukumar tattara bayanan sirri ta DSS da kuma majalisar dattawan na bogi ne.

A cewar jaridar a jiya Lahadi ministan ya amince cewa UNN ba ta taɓa ba shi shaidar kammala karatun digiri ba.

Al’amarin ya janyo cecekuce acikin al’umma musamman a kafafen sada zumunta duba da irin yadda ake hakan ya shafi ɗayadaga cikin manyan jami’an gwamnati.

By Babaji