Babaji

5698 Posts

Ɓatar tiriliyan N210: Majalisar Dattawa ta matsa bincike yayin da NNPC ya buƙaci ƙarin lokaci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawa ta bayyana cewa Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya buƙaci a ba shi ƙarin lokaci na ya fitar da cikakken bayani game da zargin ɓatar Naira tiriliyan 210 daga cikin kuɗin kamfanin tun daga shekarar 2017 zuwa 2023. Kwamitin majalisar akan asusun ƙasa (SPAC) ya bayyana haka, wanda a halin yanzu ya ke gudanar da bincike akan batun bayan da ofishin Antoni Janar ya nemi a bankaɗo rahoton kuɗin NNPC bisa zargin sauya akalar wasu maƙudan kuɗaɗe. A watan Yuli ne kwamitin ya gayyaci Shugaban NNPC, Bayo Ojulari inda ya ba…
Read More

An bayyana sunayen mutane uku da ka iya maye gurbin shugaban INEC

Shirye-shirye sun kammala yayin da Shugaban Ƙasa ya sanar da sabon shugaban Hukumar Zaɓe, INEC bayan da Farfesa Mahmood Yakubu ya kammala wa’adin mulkinsa na shekara 10 a ranar Talata. Kafin Yakubu ya sauka daga muƙamin, rahotanni sun nuna cewa Fadar Shugaban Ƙasa na nazarin mutum uku da ake hasashen za su iya maye gurbin nasa. Mutanen sune Farfesa Joash Ojo Amupitan da Mai Shari’a Abdullahi Mohammed Liman da kuma Farfesa Lai Olurode. Wata majiya daga Fadar Shugaban ƙasar ta shaida wa manema labarai cewa an kammala nazari, kuma Farfesa Amupitan ne ke kan gaba a jerin waɗanda ake hasashen…
Read More

Majalisar Dattawa ta amince da ƙwace fasfo na shekara 10 ga ƴan Nijeriyar da aka samu da laifi a ƙasashen waje

Majalisar Dattawa ta amince da haramta wa duk wani ɗan Nijeriyar da aka samu da aikata laifi a ƙasashen waje yin amfani da fasfon ƙasar na tsawon shekaru 10. Majalisar ta amince da hakan ne yayin zamanta a Abuja, ranar Talata. Sanata Abubakar Bello mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa ya gabatar da ƙudirin ga majalisar a wani ɓangare na yi wa dokar fasfo garambawul. Ƙudirin ya buƙaci a karɓe fasfo ɗin ne na tsawon shekara 10 mafi ƙaranci, lamarin da ake ganin zai taimaka wajen sanya ƴan ƙasar da ke waje kuma suke aikata manyan laifukashiga taitayinsu. Ƴan majalisar…
Read More

Ministan Kimiyya, Geoffrey Nnaji ya yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya amince da murabus ɗin Ministan Kimiyya, Ƙirƙira da Fasaha, wato Geoffrey Uche Nnaji. A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a yau Talata, ya ce shugaban ya amince da murabus ɗin Ministan, wanda ya biyo bayan zarginsa da aka yi da amfani da takardar digiri ta bogi. A ƴan kwanakin nan aka zargi tsohon ministan da yin amfani da digirin bogi daga Jami'ar Nijeriya ta Nsuka, lamarin da ya ja hankalin al'umma, duk da cewa ya musanta. Njaji ya bayyana cewa, ana masa bita da ƙulli…
Read More

INEC: Tinubu ya karrrama Farfesa Mahmood Yakubu da kyautar ƙasa ta CON

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Bola Tinubu ya amince da saukar Farfesa Mahmood Yakubu daga muƙamin Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC) bayan ƙarewar wa’adinsa na biyu kuma na ƙarshe. Sakamakon girmamawa da hidimar da ya ba wa ƙasa a muƙamin, Shugaba Tinubu ya ba shi kyautar girmamawa ta ƙasa ta "Commander of the Order of the Niger' (CON). Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata. A tsawon shekaru goma da ya jagoranci hukumar, Farfesa Yakubu ya jagoranci lamuran manyan zaɓukan 2019 da na 2023, da gabatar da sababbin fasahohi…
Read More

An karrrama Gwamnatin Kaduna bisa tallafa wa mata da iyali

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Muryar Mata (VOW) ta karrama Gwamnatin Jihar Kaduna da kyautar gwarzuwar gwamnatin bisa tallafa wa mata da iyalansu. An yi haka ne a babban taron ƙungiyar karo na 9 a Abuja, yau Talata. Baya ga gwamnatin Kaduna, an kuam karrama gwamnatocin wasu jihohi da cibiyoyi duba da irin tasirinsu wajen inganta rayukan matata da walwalar iyalansu ta hanyar damawa da su a tsare-tsare da shirye-shirye. Gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Uba Sani ta yi fice wajen nuna damuwa da lamarin kula da jinsi musamman wajen abinda ya shafi al'umma kai-tsaye da damawa da…
Read More

Farfesa Yakubu ya miƙa ragamar INEC ga Agbamuche bayan ƙarewar wa’adinsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban hukumar zaɓe (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga muƙaminsa tare da miƙa ragamar jagorancin hukumar ga May Agbamuche-Mbu, wadda za ta riƙe muƙamin a matsayin riko kafin naɗa sabon shugaba. Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne yau Talata yayin ganawa da kwamishinonin hukumar a hedikwatarta da ke Abuja. Agbamuche ita ce wadda ta fi kowa jimawa a matsayin babbar kwamishina a INEC. Ya kuma kirayi sauran kwamishinoni da daraktocin hukumar da su bai wa Agbamuche-Mbu cikakken goyon bayan kafin lokacin naɗa sabon shugaban hukumar. A watan Oktoban 2015 tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi,…
Read More

Natasha ta koma bakin aiki bayan kammala dakatarwar wata shida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a karon farko ta halarci zaman Majalisar Dattawa bayan wa'adi dakatar da ita da aka yi na watanni shida ya ƙare. A yau Talata ne majalisar ta koma bakin aiki, bayan tsawaita lokacin komarsu da ƴan makonni daga hutun da suka tafi a watan Agusta. Saidai Sanatar mai wakiltar Kogi ta Arewa ta halarci zaman majalisar ne, wadda mataimakin shugabanta, Sanata Jibrin Barau ya jagoranta a yau. Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Shugaban Majalisar kuma abokin rikicin Natasha, Godswill Akpabio bai halarci zaman majalisar ba. Dakatar da ita ya…
Read More

Kano: Shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi ya ci alwashin cigaba da tallafa wa ƙungiyar ƴan kasuwa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya ci alwashin cigaba da tallafa wa Ƙungiyar ƴan kasuwa ta Bichi Traders Multi-Purpose Cooperative Society Limited, inda ya bukaci su kasance masu haƙuri, addu’a da jajircewa bisa ƙalubalen da suke fuskanta, sakamakon sauya wa kasuwar tasu matsuguni. Alhaji Hamza Sule Mai Fata, wanda kuma shi ne Sakataren Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin ta jihar, ya kuma bayyana farin cikinsa kan ziyarar da ‘yan kungiyar kasuwar suka kai masa, inda ya ce yana alfahari da kasancewarsa tsohon dan kungiyar. A sanarwar da Jamila…
Read More

Mun kafa asusun Naira biliyan 200 don taimaka wa masana’antu da ƙananan ƴan kasuwa, inji Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kafa asusun tallafi na Naira biliyan 200 domin taimaka wa masana’antu da ƙananan ‘yan kasuwa (MSMEs) wajen ƙarfafa musu da magance matsalolin da ke hana su ci-gaba. Tinubu ya faɗi haka ne a Abuja ranar Litinin yayin buɗe taron tattalin arziƙi na ƙasa (NESG) karo na 31, inda ya ce, bayan nasarar da Najeriya ta samu na bunƙasar tattalin arziki da ya kai kashi 4.23 cikin 100 a watan Satumba 2025, sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako mai gamsarwa a fannoni da dama. Shugaba Tinubu wanda…
Read More