10
Oct
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya haɗa kai da ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan-adam kuma tsohon dan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, wajen kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Atiku ya bayyana a shafinsa na X cewa ci gaba da tsare Kanu “tabo ne ga amincin Nijeriya da bin doka da oda.” Kanu yana fuskantar tuhuma kan ta’addanci, cin amanar ƙasa, da tayar da fitina a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja — kuma tun shekaru da dama yana tsare duk da cewa kotuna da dama sun bayar da umarnin a…
