10
Oct
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗaruruwan matafiya ne suka shiga mawuyacin hali a safiyar yau Juma'a a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu bayan wani farmaki na cikin dare da mayaƙan Boko Haram suka kai wa wani sansanin sojoji a kusa da garin Ngamdu da ke da nisan kasa ƙasa da kilomita 50 daga Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe. Lamarin da ya tilasta wa sojoji rufe titin, wanda al'umma ke yawaita zirga-zirga akansa domin harkokin kasuwanci da wasunsu a yankin na Arewa maso Gabas. Shaidu da masu ababen hawa sun shaida wa manema labarai cewa, a harin ne aka yi ba-takashi…
