
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce jimillar jami’an sojoji 16 ne za a yi wa hukunci bisa zargin su da laifukan rashin biyayya da karya wasu dokokin aiki.
Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya bayyana haka a wata takarda, ranar Asabar.
Ya ce, an kama jami’an ne a yayin wani atisaye na musamman bayan gudanar da bincike akan wasu ayyuka da suka ci karo da ladabtarwar sojoji da ƙwarewar aiki.
A cewarsa, sakamakon bincike ya nuna cewa wasu daga cikin jami’an an same su ne da laifukan sakamakon ƙunci da suka tsinci kansu a ciki na rashin nasara a jarrabawar ƙarin matsayi a lokuta da dama da kuma wasu matsalolin aiki.
Ya bayyana cewa, an samu wasu daga cikinsu da maimaita aikata laifukan da ake musu shari’a akansu, lamarin da acewarsa bai dace da sharuɗɗan aikin soja ba.
Birgediyan ya ƙara da cewa, da zarar an kammala bincike akansu, za su fuskanci hukunci daidai da laifinsu bisa tsarin aikin da tabbatar da adalci.
