
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda ta ce har yanzu ba ta samu takarda a hukumance daga kotu ba kan aikin tilasta bin dokar amfani da gilashi mai duhu da jami’anta suka fara.
Benjamin Hundeyin, wato Kakakin rundunar ya bayyana haka a jiya Asabar.
Lauyan kare ƴancin al’umma, Inibehe Effiong a wani saƙo ta X, ya ce kotun ta umarci ƴan sanda da su bar batun izinin amfani da gilashi mai duhu a yadda yake.
Saidai duk da haka, Hundeyin a wata sanarwa ya bayyana cewa hukumar ba ta samu saƙo a hukumance ba akan al’amarin.
Kotun a yayin zamanta ta bayyana cewa tunda za a sake zama akan shari’ar a ranar 16 ga Oktoba, babu buƙatar fara tilasta bin dokar.
Hakan na zuwa ne jim-kaɗan da babbar kotun tarayya ta Warri a jihar Delta ta umarci rundunar da ta dakata da tilasta aiwatar da dokar.
Alƙalin da ya yi hukuncin ya umarci hukumomin ƴan sanda da su girmama ayyukan doka har zuwa lokacin da za a yi hukuncin ƙarshe akan lamarin.
