
Babbar Kotun Tarayya da ke Warri a jihar Delta, ta umarci hukumar ƴan sanda da Sufeto Janar na ƴan sanda da su dakatar da tilasta dokar amfani da gilashi mai duhu ga masu ababen hawa.
Ta ce, hana amfani da gilashin motoci masu duhu (tinted glass) ba tare da takamaiman dalili ba ya saba wa kundin tsarin mulkin ƙasa.
Kotun ta umurci rundunar ‘yan sanda da ta dakatar da aiwatar da wannan dokar.
A yayin hukuncin kotun ta bayyana cewa babu wata doka ta zahiri da ke haramta amfani da gilashin duhu ga ‘yan kasa masu bin doka.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da wani dan kasa ya shigar yana kalubalantar dokar, inda kotun ta bayyana cewa sai dai idan an samu shaidar amfani da gilashin wajen aikata laifi, amma ba a haramta shi gaba ɗaya ba.
