Daga SHEHU MUSTAPHA CHAJI
Yau kusan watanni bakwai da Engr. Rabiu Suleiman Bichi ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar kogunan Hadejia da Jama’are. Sun kama aiki tare da Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin daraktan kuɗi sai Alhaji Tijjani Isa a matsayin daraktan tsare tsare sai Engr. Baffa Datti Abdulkadir a matsayin daraktan Injiya sai Hajiya Zainab Gamawa a matsayin daraktan harkokin noma. Ana rantsar dasu suka kama aiki a take dan aiwatar da ƙudirorin hukumar da ya haɗa da kula da albarkatun ruwa dake doran ƙasa da na ƙarƙashin ƙasa a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.
Babban nasarar da suka fara samu shine na yin abinda ya dace dan daƙile ambaliyar ruwa da ke janyo asarar rayuka da albarkatun gona da dukiyoyi na miliyoyin naira kusan kowane shekara.
Bisa jagorancin Engr Rabiu Suleiman Bichi gwarzon da baya gajiya da aiki ko dare ko rana. Ko a kwananan Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi yace ” munyi aiki tare da Rabiu lokacin da nake Ministan Abuja kuma yana cikin gwarazan daraktoci a hukumar FCDA a lokacin”. Duk yayin da aka zo wa Bichi da rahoton akwai matsala a magudanan ruwa ko Kogunan dake ƙarƙashin hukumar Hadejia Jama’are a take yake bada umarnin aje a gyara. Ana kuma fara gyaran zaije wajen duk da irin yanayin wahalar zuwa ire iren waɗannan wuraren musamman da damina. Engr Rabiu Suleiman Bichi da kansa ya kan hau babur ko kwale kwale da shiga chaɓi da taɓo dan ya tabbatar anyi aikin. Wannan sadaukarwan ne dalilin daƙile hambaliyar ruwa a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi a wannan shekarar. Kuma kasancewar ƙofar sa kullum a bude yasa ma’aikatan hukumar duk yayin da suka hango matsala za su kira shi kai tsaye dan sanar dashi. Shi kuma a take ya umarci injiniyoyi su garzaya wajen dan gyara.
Ƙudirorin shugaba Tinubu na samar da abinci yayi wa Engr Bichi tasiri sosai. Hakan yasa yana cikin aiki ba dare ba rana domin wannan ƙudiri na Shugaba Tinubu ya zama ya tabbata domin ragargazan yunwa da samar da dubbin arziki.
Shugaba Tinubu ya bada umarnin gyara da ƙara girman Dama Damai har 16 a Jihar Kano ciki har da Dam ɗin Tiga da Dam ɗin Challawa Gorge da Dam ɗin Kafin Chiri. Gyaran waɗannan Dama Damai zai taimakawa manoma fiye da 30,000 su da iyalan su. Sannan za’a sami sabbin ƙarin heka 50,000 dan noman rani. Manoma kuma zasu rinka noma sau uku a shekara. Kuma wannan gyaran da ƙara girman Dama Damai zai samar da sabbin ayyukan yi har 300,000.
Bichi da tawagar sa a kullum suna aiki tuƙuru tsakanin jihohin Kano da Jigawa da Bauchi domin tabbatar da manoma suna samun isashen ruwa dan bunƙasa noman damina dana rani. Kuma sun ƙaddamar da yaƙi kan ciyawar kachala dake taimakawa wajen jawo ambaliya da hana manoma samun isashen ruwa dan kulawa da shukokin su.
Wasu daga cikin ayyukan cigaba da hukumar Hadejia Jama’are ta samu ƙarkashin jagorancin Engr Rabiu Suleiman:
1) Bunƙasa noman zamani da jawo al’umma musamman matasa su shiga harkan noma dan tabbatar da nasarar shugaba Tinubu na samar da abinci.
2) Tsari da shirin baiwa matasa 5000 horo a fannonin noman zamani musamman a fannin noman rani da kiwon zuma da noman a ɗakunan zamani. Burin Engr. Bichi ana samar da matasa da zasu zama hamshakan attajirai 5000 a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi kusan kowane shekara.
3). Bunƙasa noman rani ta hanyar ƙara heka da ake noma a yanzu daga heka 54,000 zuwa heka 540,000. Hakan zai ƙara bunƙasa noman shinkafa daga tan 206,000 zuwa tan miliyan ɗaya.
4). Samar da hanyoyin da za’a sami ƙarin ruwa da kashi 20 dan bunƙasa noman rani.
5) Engr Rabiu Suleiman Bichi ya kasance ya aminta da da’awar matar shugaban ƙasa Sanata Oluremi Tinubu na noma a kowane gida. Wannan ƙudirin nata zai taimaka wajen samar da abinci.
6) Manoma su riƙa noma har sau uku ko fiye a shekara a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.
7) Yanke Ciyawar Kachala ko wane lokaci a shekara da saka masana su kirkiro hanyar da za’a rika amfani da Ciyawar a matsayin makamashi a gidaje.
8) Kulawa da gyaran mugudanan Ruwa.
9) Ɗaukan matakai dan daƙile ambaliyar ruwa da zaizayan ƙasa.
Hukumar Haɗejia Jama’are ƙarƙashin jagorancin Engr Rabiu Suleiman Bichi sun dau alwashin gyara wuraren na musamman da aka tanade su dan tara ruwa domin noman rani. Wasu wuraren tara ruwa sunyi shekaru masu yawa a lalace ko ba’a amfani dasu. Ma’aikatar hukumar Hadejia Jama’are suma suna cikin annashuwa domin sun sami Shugaba da zai farfaɗo da inda suka kwashe shekaru suna aiki .
Muna amfani da wannan damar dan kira ga Engr. Rabiu Suleiman Bichi ya nemi miƙa roƙon Kanawa ga Shugaba Tinubu ya sahale a samarwa Kano gidan ruwa na zamani kamar wanda akeyi a yanzu a Dutsen Jihar Jigawa da Abuja dan kawo karshen matsalar rashin ruwan amfanin yau da kullum a gidaje.
Saboda amincewa da girma da kima da al’umma ke gani na Engr. Rabiu Suleiman Bichi mutane da dama sun zama manoma a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi wanda hakan zai bunƙasa harkan noma.
Ƙudirin Shugaba Tinubu na samar da abinci zai zama gaske bisa jagorancin Engr Rabiu Suleiman Bichi a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.
